Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

Muhimmancin alqawari da illolin karya shi

2016/04/05

Muhimmancin alqawari da illolin karya shi

Muhimmancin alqawari da illolin karya shi

 

Cika alqawari yana daya daga cikin al\'amuran rayuwa da ya doru a wuyan mutum. Dabi\'ar mutum ne ko da wane addini ya ke bi; ya ji bacin rai idan ya karya alqawari, murna da farin ciki kuma su kan lullube shi idan har ya cika alqawarinsa, sawa\'un wani mutum qwara daya tal ya cika wa alqawarin, ko kuma al\'umma baki dayanta. Irin tarbiyyar da aka taso da mutum a cikinta tana taka rawar a-zo-a-gani a halayyarsa da za su biyo baya. Dan haka ne wajibcin yin tarbiyya tagari da kiyaye dorewarta da nesantar abubuwan da za su lalata halin mutum ya zama abu ne da babu ka-ce-na-ce a kai. Kyakkyawar tarbiyya ita ce mabudin kamalar halayen qwarai.

Mutunci ya wajabta cika alqawari ko da kuwa na baki wanda aka qulla tsakanin bangarori biyu, ko da kuwa babu wata rubutacciyar hujja. Karya alqawari yana jawo ficewa daga da\'irar daraja da mutunci. Qetare haddin wa\'adin da aka yi alqawari shi ma rashin mutunci ne.

Buzarjumehr yana cewa:

"Karya alqawari yana matuqar nesanta tsakanin mutum da mutunci."

 

Duk wanda ke kauce hanya madaidaiciya, ta hanyar karya alqawari cikin sauqi to yana shuka kangarewa ne da qyama a zukatan wasu. Sannu-sannu mai karya alqawari zai kunyata ya yi qoqarin nade tabarmar kunyarsa ta hanyar kame-kamen dalilai da warware tufkar da ya yi, har daga qarshe mutane su gane cewa dai shi dama mutum ne batacce munafuki.

Babu shakka karya alqawari yana daga cikin abubuwa mafiya saurin kawo tangarda a al\'umma da raunana dangantaka a tsakanin jama\'a. Tabbatacce ne al\'ummar da ke cike da gardandami da rashin yadda za ta sukurkuce a tsarin zaman jama\'arta, kuma sakamakon haka mutane ba za su taba yarda su amince da kowa ba hatta danginsu na kusa.

Akwai wasu irin mutane da ba wai kawai suna yi wa alqawari riqon sakainar kashi ba ne a\'a, har ma tsammani suke yi karya alqawari wayo ne da iya shirya bilhu. Bilhasali ma har alfahari suke yi da aikinsu.

 

Cika alqawari yana da muhimmanci ga wanda yake qaunar ya zauna a cikin jama\'a, shi ne kuma tushen farin cikin zaman tare da ci gaba da cin nasara.

An ruwaito cewa an kamo wasu jama\'ar Hawarijawa a zamanin Hajjaj ibnu Yusufus Saqafi, aka kai su gurinsa dan ya duba al\'amarinsu. Sai Hajjaj ya hukunta yadda ya so. Yayin da mutum na qarshe ya gurfana a gaban Hajjaj dan ya saurari hukuncin da za a yanke masa sai lokacin salla ya yi. Da Hajjaj ya ji an qwala kiran salla sai ya danqa mutumin ga wani na hannun damansa yace masa ya kawo shi da safe.

Sai mutumin ya fita daga fadar tare da fursunan. Suna cikin tafiya sai fursunan ya ce; "Ni fa ba na daga cikin Hawarijawa kuma ina roqon Allah cikin RahmarSa Ya bayyana rashin laifina a sarari, domin an tsare ni ba laifin tsaye ba na zaune." Sannan yace "ina roqonka dan ka bani izini in je in kwana a tsakanin iyalina, matata da \'ya\'yana ko na samu na ba su wasiyyata. Na yi alqawarin cewa zan dawo da asubar fari kafin zakara ya yi cara." Bayan mutumin ya yi shiru na dan lokaci sai ya amince da buqatar fursunan saboda tsanantawar da ya yi, ya sallame shi ya tafi na tsawon wannan daren.

Jimkadan sai mutumin ya fara fargaba yana jimamin cewa Hajjaj zai huce haushinsa a kansa. Can tsakar dare sai mutumin ya farka yana ta jin tsoro amma abin al\'ajabi sai ya ji fursunan na da ya ba wa izinin ya tafi gida ya komo yana qwanqwasa qyauren qofar gidansa. Sai mamaki ya cika shi ya ce kuma bai iya gimtsewa ba sai ya ce:

"Me ya kawo ka qofar gidana?"

Sai fursunan ya ce: "Duk wanda ya yi imani da girman Allah da QudurarSa, kuma ya sanya Shi shaida a kan alqawarinsa; to dole ne ya cika alqawarinsa."

Sai mutumin ya wuce da fursunan kai tsaye zuwa fada, Hajjaj ya shahara wajen rashin tausayi amma sai da gaskiyar wannan mutumin ta yi tasiri a kansa har ya sake shawara. Ya qudiri aniyar zai sake shi, can sai ya juya ga mutumin nan da ya kawo shi ya ce kana so in ba ka kyautar wannan kamammen? Sai mutumin ya ce idan ka yi haka kuwa ai da na so qwarai. Sai ya ba shi kyautar sa; shi kuma yana fita daga fada sai ya sake shi ya yi tafiyarsa.

 

Mu qaddara cewa akwai wani kamfani na kasuwanci wanda ba ya kiyaye qa\'idodinsa, wannan babu inda zai kai shi illa ga rashin amincewa a gurin mutane da kuma karyewar kamfanin.

Babu wani abu da zai qarfafa al\'umma ta kankama gargar kamar amincewa da juna a tsakanin jama\'a. Alaqa tsakanin mutane ba za ta kankama ba, zukata ma ba za su amince da juna ba sai har idan kowane mutum ya dauki maganarsa da muhimmanci kamar yadda yake ba wa qa\'idodi da dokokin hukumar qasa muhimmanci, kamar yadda tajiri zai damqa kayansa ga abokin cinikinsa, mabaraci kuma zai biya kudinsa ga wanda ya ba shi bashi da dai sauransu, ta haka ne kawai za a warware rikice-rikice, kuma rayuwa ta miqa yadda ya dace.

Dan haka abin da ya fi dacewa ga mutum shi ne ya jinjina qarfinsa tukuna kafin ya qulla wani alqawari kuma ya nesanci qudira duk wata yarjejeniyar da ba shi da ikon zartarwa. Idan mutum ya yi alqawari ya zo bai cika ko da a sakamakon gazawarsa ne; duk da haka dai nauyin a wuyansa ya rataya. A bisa dabi\'a shi za a zarga da suka.

 

Musulunci ya hana karya alqawari

Ya kamata mutum ya tsara shigi da ficensa ya zama ya dace da hankali domin sauran jama\'a su sanya shi a sahun masu hankali. Muwafaqar al\'umma ta dogara ne kaco-kam akan hadin kan dai-daikun mutanenta. Dan haka tilas ne kowa ya tsara rayuwarsa ta dace da gaskiya da haqiqa. Sa\'an nan ya guje wa abin da zai haifar da rashin hadin kai da munafunci matuqar iyawarsa. Idan har aka qullaalqawari da kiyaye shi a bisa asasin imani da halayyar qwarai da karimci to shi ne mafi dorewa kuma mafi qarfi.

Addinin musulunci ya kushe karya alqawari matuqa gaya; yadda bai yi sassauci ba ko kadan ga mabiyansa da su karya alqawari ko da kuwa tsakaninsu da fasiqai ko fajirai ne.

Imam Baqir (AS) yana cewa:

"Abubuwa uku Allah Bai yi sassauci ga kowa ba a kansu: kiyaye Amana ga mutumin kirki da fajiri, da cika alqawari ga na kirki da fajiri da bin iyaye na kirki ne su ko fajirai.

(Littafin Alkafi juz\'i na 2 shafi na 169)

 

Alqur\'ani kuma ya sifanta masu imani da cewa:

"... wadanda su masu kiyaye amanarsu ne da alqawarinsu..."

(Surar Muminun: 8)

 

Kazalika ya yi kira ga musulmi da su cika alqawarinsu, yace:

"Kuma ku cika alqawari, lalle alqawari abin tamabaya ne a gare shi."

(Surar Isra\'ila: 244)

 

Manzon Allah (SAWA) ya qidaya karya alqawari daga cikin alamun munafunci yana cewa:

"Akwai abubuwa hudu duk wanda yake da su to munafuki ne, idan kuwa yana da daya daga cikinsu to yana da alamar munafunci, har sai ya rabu da shi, wato idan ya yi magana sai ya tsuga qarya, idan ya yi yarjejeniya sai ya sa6a, idan ya qulla alqawari sai ya karya, idan kuma ya yi husuma da wani sai ya zunqe."

(Littafin Biharul anwar, juz\'i na 15, shafi na 234)

 

Imam Ali (AS) ya rubuta a cikin wasiyyar da ya yi wa Malik Ashtar cewa:

"Ka kiyayi gori ga talakawanka, saboda alherin da ka yi musu, ko kuma ganin yawan abin da ka aikata ko kuma ka yi musu alqawari sa\'an nan ka biyo bayan alqawarin naka da sa6awarka, domin gori yana 6ata kyakkyawan aiki, ganin yawan aikinka kuma yana dushe hasken gaskiya, sa6awar kuma ya na jawo qyama daga Allah da mutane. Allah subhanahu wa Ta\'ala Yana cewa: Babban abin qyama ne a gurin Allah ku fadi abin da ba ku aikatawa."

(Littafin Mustadrikul wasa\'il juz\'i na 2, shafi na 85)

 

Ali (AS) ya qara da cewa:

"Cika alqawari dan tagwayen gaskiya ne ni ban san wata garkuwa fiye da shi ba."

(Littafin Gurarul Hikam shafi na 228)

 

Addinin musulunci ya ba da muhimmanci matuqa ga tarbiyyar yara. Ya bayyana wa iyaye tilascinsa na halayyar qwarai filla-filla ta hanyar qwararan tafarkuna masu gamsarwa. Matuqar iyaye ba sa kiyaye abin da ya kamace su ba dangane da halayen qwarai to ba za su iya koya wa yaransu riqo da halayen qwarai ba. Domin aiki ya dara batun-baka. Saboda haka ne Manzon Allah (SAWA) ya hana iyaye karya alqawarinsu ga \'ya\'yansu, yace;

"Kada wani mutum ya yi wa dansa alqawari sa\'an nan ya karya."

(Littafin Nahjul fasaha shafi na 201)

 

Dakta Alindi kuma yace:

"An kawo mini wani saurayi dan shekara goma sha shida, da ya kan yi sata kullu yaumin, dan in yi masa magani. Sai na gano cewa a lokacin da yaron yake dan shekara bakwai ko takwas babansa ya ta6a tilasta shi ya ba wa \'yar tajirin da yake masa aiki abin wasansa. Wannan abin wasa kuwa a gurin wannan yaro shi ne abu mafi qima da daraja domin sai da ya qare dukkan qoqarinsa ya wahala sa\'an nan ya same shi. Mahaifin yaron ya yi alqawarin zai saya masa wani ya bashi a madadin waccan amma sai ya manta ba da nufinsa ba. Dan haka yaron bai ga mafita ba illa ya saci \'yar cakuleti daga aljihun babansa domin ya dau fansa. Daga nan bayan kwana daya sai ya kurda gidan maqwabta ya fasa gilashi ya sato wani abu. Dan haka warkar da wannan yaro ba ta yi mini wahala ba, na ci nasara a kan haka. Uban wannan yaro shi ne ya shigar da shi wannan hanya sabili da ya yi wa dansa ba daidai ba, kuma idan da ba dan an magance al\'amarin da wuri ba kuma sosai ba, har ya ci gaba da yin haka, to da yaron yana iya zamowa wani riqaqqen ma6arnaci mai hatsari, alhali yana da damar wata rana ya zamanto babban mutum mai hankali da qarfin himma." (Littafin Ma wa farzandan ma)

 

Imam Ali (AS) yana cewa:

"Idan ka sami amini to ka zama bawa gare shi, kuma ka tabbatar masa cika alqawari da gaskiya tare da yarda."

(Littafin Gurarul Hikam shafi na 223)

 

Mutanen kawai da suka cancanci zaman tare da samun qaunar jama\'a, sune masu kyawawan sifofi da falalar \'yan Adamtaka. Manzon Allah (SAWA) yana cewa:

"Mafi alherin mutane shi ne wanda ya shaqu da mutane masu daraja, wanda ya yi mu\'amala da mutane bai zalunce su ba, wanda ya yi magana da su bai yi musu qarya ba, wanda ya yi musu alqawari bai sa6a musu ba, to shi yana daga cikin wanda darajarsa ta kammala, adalcinsa kuma ya bayyana, kuma ya wajaba a yi \'yan uwantaka da shi."

 

Dakta Smiles yana cewa:

"Idan kuka zauna tare da mutane masu tsarkin ruhi da halayyar qwarai, za ku ji wani abu yana jan zukatanku da halayenku zuwa ga kyautatuwa da daukaka. Zama da mutanen da ke da qaqqarfan hankali masu falala, gogayya ce babba wadda ta dara kome qima da tsada. Domin zama da su irin wadannan mutane ya kan ba mu sabon qarfin ruhi, ya koya mana hanyoyin rayuwa da ladubbanta, ya gyara ra\'yoyinmu da tunaninmu dangane da wasu. Tun da yake su sun fi mu qarfin ruhi da tsarkin zukata sai mu amfana da zama tare da su mu kyautata halayyarmu, manufofin rayuwarmu kuma su daukaka su taimake mu a ayyukanmu wajen taimaka wa sauran jama\'a. Zama da mutanen qwarai na cusa mana alheri da kyautatuwa, halin qwarai tamkar haske ne yana haskaka duk abin da ke gewayensa da wanda ke kusa da shi."

(Littafin Akhlaq)

 

Abubuwan da muka ambata can baya sun tabbatar mana kenan cewa ya kamata kowane mutum ya san nauyin da ya rataya a wuyansa dangane da alqawari da rantsuwa.

 

Wannan bahasi mun kawo muku shine daga rubutun fitaccen malamin nan Sidi Mujtaba Musawi Lari