Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

sakamako da Ribar Kyakkyawan Zato

2018/02/27

sakamako da Ribar Kyakkyawan Zato

Sakamako da ribar kyakkyawan Zato

Kamar yadda cututtuka iri dabam-dabam suke nakasa jiki, haka miyagun dabi\'u da munanan sifofi suke lalata nutsuwa da tunani. Duk da qarfin da kwanya take da shi tana buqatar agajin kyawawan dabi\'u. Mutum ya kan ji farin ciki idan yana da kyawawan dabi\'u, kazalika kuma idan dabi\'un nasa suka zama bai daya da tunanin sa. Saboda haka wajibi ne mutum yayi himma ya kankare munanan dabi\'un da suka lullube rayuwar sa ya musanya su da kwanciyar hankali da nutsuwa.

Daya daga cikin abubuwan da ke ba da kwanciyar hankali shine fata na gari a rayuwa da kuma yarda da jama\'a. Fata na gari da kyakkyawan zato ga mutane suna samar da nutsuwa, sabanin mummunan fata da mugun zato ga jama\'a, wadanda ke dushe tunani su tsimburar da kamalar sa. Fata na gari a rayuwa kamar haske ne a cikin duhu, yana fadada tunani kuma ya qara wa mutum son alheri, ta haka har zai ci gaba a fahimtar sa game da rayuwa da ra\'ayin sa game da ita. Sai ya gane kyawun rayuwa da dadin ta kuma ya dinga ganin mutane da daraja yana mutunta su sosai.

Sakamakon haka sai damuwar sa ta ragu, tsammanin alherin sa ya qaru, kuma dangantakar sa da jama\'a ta qara qarfi sosai a zuciya da kuma a zahiri. Babu wani abu da ke fitar da mutum daga qunci da damuwar rayuwa kamar fata na gari. Duk wanda yake da wannan zababben hali na qwarai ba wai kawai a lokacin zaman lumana ne yake da nutsuwa ba, a\'a ko da a cikin arangamar al\'amuran yau da kullum ne yakan kwantar da hankali ya bi komai cikin nutsuwa ya warware shi ta hanyar aiki da hankali cikin sauqi. Kuma shi da\'iman yana cikin annashuwa ne da nutsuwa da kwanciyar hankali.

A rayuwa larura ne mutun ya yi abin da zai sa jama\'a su amince da shi. Dole ne fata na gari ya yawaita a tsarin zaman tare wajen yardar da mutane. Jin hakan kuwa na tasiri a samun sa\'adar daidaiku da kuma al\'umma baki daya. Amincewa da juna a tsakanin jama\'a za ta jawo ci gaban al\'umma, alhali rashin amincewa kuwa zai jawo dakushewa da lalacewar al\'umma. Duk yayin da dangantakar jama\'a ta qara qarfi ta qara kyau to la-budda ci gaban al\'ummar ma zai qara qaimi ya habaka. Babbar ribar fata na gari ita ce hade kan jama\'a da sa taimakekeniya da yarda da juna a tsakanin su.

Idan aka assasa zama da juna a bisa alaqar zukatan juna, amincewa da kuma yiwa juna kyakkyawan zato, to haqqan za a zauna cikin farin ciki kuma a yi zaman lafiya. Amma matuqar babu kyakkyawan zato ga juna a tsakanin jama\'a zukata kuma suka cika da shakku da zargin juna, ba zai yiwu a sami taimakon juna a tsakanin su ba, hasali ma sai suyi ta muzgunawa da cakar juna babu gaira babu dalili. Al\'ummar da ke cike da irin wannan hali kuwa holoqo ce ba ta da wani abin kuzo ku gani irin na sauran al\'ummu. Wani malami yace: "Kyakkyawan zato yana daga imani, babu wani aiki da zai yiwu idan babu imani da kyautata zato."

Gwargwadon yadda mutum ya amince da mutane suma kimanin yadda za su amince da shi ke nan, domin yadda kayi haka za a yi maka, a kowace al\'umma ne kuwa. Amma kada mu manta da cewa akwai wagegen bambanci tsakanin fata na gari da yin kyakkyawan zato ga wasu. Ko kadan ba kyakkyawan zato bane haka kawai mutun bai san wani ba ya miqa masa wuya a rana tsaka, ya bi duk abin da ya fada sau da qafa ba tare da bincike da aunawa ba. Har ila yau bai kamata mu yi wannan zato ba ga wanda ya shahara wajen aikata sabo a bayyane. A taqaice dai ba koyaushe ne ake yi wa kowa kyakkyawan zato a kowane hali ba. Mutum mai kyautata zato da yiwa ayyukan mutane kyakkyawar fassara ba wai galantoyi ba ne, da\'iman ya na lura ne da kyakkyawan qarshen al\'amura. Dan haka yana taka tsantsan a kaiwa da komowarsa kuma yana kyakkyawan nazari da tunani a ayyukan sa.

Gurin da aka samo:

Littafin kyawawan dabi\'u na Sidi Mujtaba Musawi Lari.