Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

Musulunci ya yi Umarni da Kyakkyawan Zato

2018/03/19

Musulunci ya yi Umarni da Kyakkyawan Zato

Musulunci yana umarni da kyakkyawan zato.

   Addinin musulunci ya umarci Musulmi da su yi wa junansu kyakkyawan zato kuma su yi wa ayyukan mumini kyakkyawar fassara wadda ta dace da shari\'a. Bai halatta ba wani ya dauka cewa wane fasiqi ne matuqar bai tabbatar da qaqqarfar hujja ba.

Imam Ali (AS) yace:

"Ka dauki al\'amarin dan uwanka a matsayi mafi kyau har sai wani abu da zai sa ka janye ya bayyana a gare ka, ka da ka yi mummunan zato ga kalmar da ta fito daga bakin dan uwanka alhali za ka iya yi mata kyakkyawan zato."

Littafin Jami\'us Sa\'adat, Juz\'i na 2, shafi na 28

Yi wa juna kyakkyawan zato yana qulla qauna a tsakanin jama\'a kuma ya samar da hadin kai a tsakanin su. Shugabannin musulunci sun yi bayanai iri-iri dangane da sakamakon kyakkyawan zato. Imam Ali (AS) yana cewa:

\'Duk wanda ya yi kyakkyawan zato wa mutane to za su so shi."

Littafin Gurarul Hikam

Dokta Marden yace:

"Idan za ku yi abota da wani, to ku yi qoqari ku dubi kyawawan halayen sa da dabi\'un sa na qwarai kawai. Sa\'annan kuma kuyi qoqari ku mutunta wadannan halaye nasa a zuciyar ku. Idan har kuka yarda da wannan wasiyya tawa kuka riqe ta a zuciyar ku to za ku yi zaman lafiya da kowa kuma kowa zai yi sha\'awar qulla abota da ku."

Littafin Pirozi Fikr

Kyakkyawan zato da amincewa da jama\'a na iya canja hatta tunanin wadanda suka dulmiye a cikin zunubi ma. Yazo a littafin Gurarul Hikam shafi na 378 cewa Imam Ali (AS) yana cewa:

"Kyakkyawan zato yana kubutar da wanda ya dulmiya a cikin aikata zunubi."

Dakta Dale Carnegie yace:

"Na gana da shugaban qungiyar masu hotel wadda aka assasa ta a shekarar 1885. Adadin hotel-hotel din da ke cikin wannan qungiya, ashirin da shida ne, ana gudanar da ayyukan wadannan hotelolin ne ta wata hanya ta musamman da ake kira, \'mu\'amalar ban girma\', a wadannan hotelolin ba a kebe wani mutum na musamman don yin lissafin kudin abinci ba. Duk mai son abinci zai shiga ne kai tsaye ya fadi irin wanda yake so kuma a bashi, illa iyaka shi ne zai duba bill din kudin ya ga yadda ya kama bayan ya ci ya sha, kuma in ya zo fita sai ya ba da kudin ga mai lura da asusu, ya yi tafiyar sa ba tare da wani ya yi masa qididdiga ba cewa shin daidai ya biya ko a\'a.

Sai na yi wuf nace wa shugaban wannan qungiya, tabbas dai kuna da dan sandan ciki ko? Domin ba zai yiwu ku amince da duk mutanen da ke zuwa nan dan cin abinci ba. Sai shugaban ya kada baki yace da ni, Af! Ai mu ba ma gadin masu cin abinci domin mun yi imani da cewa aikin da muke yi gabadayan sa mai kyau ne, ba don haka ba, da ba mu ci gaba da gudanar da shi haka har na shekara hamsin ba. Duk masu zuwa cin abinci a nan sun san cewa ana yi musu ma\'amalar ban girma ta masu karimci, dan haka kowa daga cikin su, faqirin su da mawadacin su, barawon su da mabarnacin su qoqari yake ya ga ya zamo daidai da kyakkyawan zaton da ake yi masa a nan."

Mista Louis liktan dabi\'un \'yan Adam yace:

"Idan kuna tare da qidahumin mutum mai tabargaza a shigi da ficin sa, idan har kuna so ku dawo da shi kan hanyar alheri to kuyi qoqari ku sa ya fahimci cewa kun amince da shi kuma ku yi masa mu\'amalar mutunci da karimci, in har kun yi haka, da sannu za ku ga yana rikedewa dan ya zamo amintacce saboda amincewar da ku ka yi da shi. Har ila yau kuma zai yi ta fadi-tashi dan ya dace da zaton da kuke yi masa na alheri da mutumci."

Littafin A\'iyne Dostyabi

Dokta Gilbert Roben ya rubuta cewa:

"Ku gaskata yara. Wato kuyi mu\'amala da su tamkar ba su taba aikata wani kuskure ba. Abin nufi shine ku mance da abin da ya riga ya wuce. Ku dorawa gantalalle daga cikin su, ko laqwasono, ko qazami a taqaice dai duk wani mai baudewa daga sahun jama\'a a cikin su, a dora masa muhimmin aiki sa\'annan a lura da shi, a qarshe za a ga ya gyaru ya zama na gari. Abin da zai jawo haka kuwa shine, yarda da aka yi da shi. Amincewa da kyautata mu\'amala suna iya kawar da cikas din da ke iya hana ruwa gudu. Dan haka, wasu ayyukan katobara gyaran gangar auzunawa ke jawo su."

Yal  Bint yana ganin cewa babu wata hanyar da za a iya raba yaro barawo da dauke-dauke illa a tila masa amanar kudi, talalabo (rago) kuma a nannaga masa aiki daidai qarfin sa ko ya zama mai kuzari.

Kyautata zato yana kwantar da hankalin mutum.

Imam Ali (AS) yana cewa:

"Kyakkyawan zato hutun zuciya ne kuma kubutar addini ne."

Littafin Gurarul Hikam shafi na 376

Kyakkyawan zato magani ne mai warke zulumin al\'amuran rayuwa na yau da kullum. Ya zo a littafin Gurarul Hikam shafi na 377 cewa Imam ali (AS) yana cewa: "Kyakkyawan zato na rage zalama".

Dr. Marden na cewa:

"Babu wani abu da zai sa mu ga kyawun rayuwa kuma ya rage mana dacin ta, ya buda mana hanyar muwafaqa kamar kyakkyawan zato. Ku ji tsoron mummunan zato kamar yadda ku ke tsoron cututtuka da jafa\'i. Ku bude qwaqwalwar ku ga kyakkyawan zato za ku yi al\'ajabin yadda za ku tsira daga munanan tunane-tunane cikin sauqi".

Littafin Piroz Fikr

Lalle ne mu\'amalar musulmi ta zamo ta yi nesa da mugun fata da mummunan zato a tsakanin su. Dan hakane Imam Ali (AS) yake wasici, inda yake cewa a kyautata mu\'amala a tsakanin juna. Matuqar jama\'a suna yi maka kyakkyawan zato; to kada ka aikata abin da zai sa su ga tsiraicin ka har ka basu kunya.

"Duk wanda ya dogara da kai yana maka tsammanin alheri to lalle yayi maka kyakkyawan zato, dan haka kada ka sabawa zaton sa".

Littafin Gurarul Hikam,  shafi na 680

Har ila yau ya nuna cewa zato alqalin hankali ne, inda yace;

"Zaton mutum shine mizanin hankalin sa, aikin sa kuma shine kyakkyawan shaida a kan asalin sa".

Littafin Gurarul Hikam shafi na 474

Idan zaton wani game da mutane mummuna ne, to babu shakka hankalin sa ma haka yake. Kore mummunan zato game da wani daga zuciya kyakkyawan dalili ne da ke nuna qarfin zuciyar wanda ya aikata hakan, Imam Ali (AS) yana cewa:

"Wanda yayi watsi da mummunan zato game da wani, to hankalin sa lafiyayye ne, zuciyar sa kuma nutsattsiya ce".

Litaafin Gurarul Hikam  shafi na 676

Samuel Smile yace:

"Ya tabbata cewa duk wani mai qarfin himma da yalwar qirji, farin ciki da tsammanin alheri ne dabi\'ar sa a rayuwa. Da\'iman yana lura da kowa cikin nutsuwa da sanin ya kamata. Komai tsananin duhu ma\'abota hankali suna ganin haske su kuma bi shi, kome rintsi da rikitarwa kuma suna rarrabe alheri su bi shi. Dan haka su, kome bala\'i da musiba sai su qara qarfi, kome qunci da baqin ciki kuma sai su qara dauriya da fahimta da ilmi. Dabi\'a irin wannan alheri ce da wadda ta kamata sahibin ta ya riqe ta da kyau. Masu irin wannan dabi\'a koyaushe suna cikin annurin fuska da fara\'a, zukatan su kuma suna cike da haske tamkar wata daren sha biyar. Duk inda suka fuskanta sai su haska shi tarwai ya rikida, ya zamo irin launin da suka so daga cikin launuka".

Imam sadiq (AS) ya nuna cewa kyautata zato, haqqin musulmi ne akan musulmi dan uwan sa, inda yace:

"Yana daga haqqin mumini akan mumini... kuma kada ya qaryata shi".

Littafin Usulul kafi, Juz\'i na 1, shafi na 394

Qarfin imani shi ne abu mafi muhimmanci wajen samar da kyakkyawan zato. Idan har mutane suna da cikakken imani to tabbatacce ne cewa za su amince da juna. Cutar rashin isasshen imani itace take tumbuke kyakkyawan zato ta dasa mummunan zato a gurbin sa. Musulmi na qwarai mai cikakken imani mai zaton alheri mai tawakkali, duk yayin da ya fahimci cewa ya gaza, nan da nan sai ya mayar da al\'amarin sa ga Allah, ya riqe shi da tsarkakakkiyar zuciya alhali yana riqo da halaye na qwarai, har ya kai ga samun canji cikin sauqi.