Gajerun labarai masu dauke da darusa kashi na 3
ALQALI
An taba samin wani alqali A\'dilin gaske. da yazo mutuwa, sai yayiwa matar Shi wasicci da cewa, idan ya mutu, bayan anyi mashi wanka, to kada a rufeshi, yana so a Dora shi akan gadon katako, zuwa wasu \'yan kwanaki, aga me zai faru ga jikin shi, ya ci gaba da cewa, shidai ya san baiyi wasu munanan ayyuka ba (kuma dama an shaide shi cewa Adili ne). Da ya mutu sai matar nan tayi kamar yadda ya umarceta, bayan Dan qanqanin lokaci, sai taga tsutsotsi suna cin qwaqwalwarshi, sai tayi mamaki matuqa.
kashegarin ranar, sai tayi mafarkin mijin nata, yana ce mata, kinyi mamakin abin da ya faru ga jiki na ko? tace qwarai ma kuwa? sai ya ce mata, hakan ya faru ne, sakamakon wata rana da qanin matarshi suka yi fada da wani, da aka kawo qarar gabanshi, sai a zuciyar Shi, ya raya cewa Allah yasa qanin matar nashi dinnan ya zama shine mai gaskiya. kuma a al\'amarin ya kasance shine mai gaskiya din. To shine dalilin faruwar haka ga jikinshi, KAWAI DAN YAJI A RANSHI CEWA, INAMA ACE MAKUSANCIN SHI YA KASANCE MAI GASKIYA!!!
GASKIYA DOKIN QARFE
Anyi wani sarki a zamanin da, Wanda alqalinshi yana da wani Dan\'uwa mumini mai gaskiya da matar shi, itama mumina qwarai. Sai Wata rana sarkin ya nemi a samo mashi wani mutun amintacce, yana so zai tura Shi wani gari domin wani aiki na musamman, sai ya buqaci Alqalin nan da ya samo mashi, sai alqalin nan yace yana ganin ba Wanda ya dace a tura sai wannan Dan\'uwan nashi.
Dan haka sai ya kira shi, ya sanar dashi abin da sarki ya buqata, Amma sai Dan\'uwan nan nashi yaqi amincewa, yace gaskiya ba zai iya barin matarshi ita kadai ba. sai alqalin ya dage, yana ce masa, sarki yana matuqar so ya ga kaine kaje wannan aiken, da ya dage dai akan yaje, sai Dan\'uwan yace, to tunda ka takura sai nine zan yi wannan tafiya, to ya zama wajibi ka Kula min da Mata ta, da kula da duk ayyukan da take buqata, har dawowata.
Da alqali ya amince da haka, sai yayi shiri ya tafi aiken sarki, yayi sallama da matarshi, duk da cewa itama ba tayi murna da wannan tafiya ba. Daga nan sai alqali ya rika zuwa gurin matar yana yi mata aike-aiken da ta buqata, kamar yadda Dan\'uwanshi ya buqata, ana haka sai ya Kamu da sonta, har ta kai ga ya neme ta da lalata, amma taqi amincewa.
Amma sai alqalin nan mai cike da son zuciya, yayi mata barazana da cewa, ko ta yarda da buqatarshi, ko kuma yaje yayi rantsuwa a gurin sarki yace tayi zina. Ita kuma taqi, tace yayi duk abin da zai iya yi, Amma ita dai ba zata taba sa6awa Allah ba, kuma ba zata ci amanar mijinta ba. Ganin haka sai alqalin nan yaji tsoro idan Dan\'uwanshi ya dawo ya sami labarin abin da yayi niyyar yiwa matarshi, dan haka sai ya tafi wajen sarki ya gaya masa cewa matar Dan\'uwanshi ta yi zina, kuma ya bincika, ya tabbatar da hakan. Shikenan sai sarki yace, to ai sai aje a jefe ta.
Sai alqali ya tafi gurin ta ya sanar mata cewa, naje na gayawa sarki, kuma yace a jefe ki, Dan haka idan baki bani hadin kai ba, to zan yi qoqari in ga cewa an jefe ki kin bar duniya. Sai matar nan ta sake cewa, kayi duk abin da Kaga za kayi, ni dai ba zan ta6a amsawa mummunar buqatarka ba. shikenan sai alqali ya hada mutane aka tafi jeji akayi dan rami aka zaunar da ita a ciki, sannan aka yi mata ruwan duwatsu a ka, har sai da yaga cewa ta mutu, sannan suka dawo gida.
Can da tsakar dare, ashe da sauran numfashinta, sai ta farfado, ta girgije duwatsun kanta, ta fito waje, cikin tsananin azaba da wahala ta isa qofar wani gurin bautar wani malamin (faada) yahudu, ta fadi anan sai bacci a wannan gurin, sai da safe malamin yahudun nan ya bude qofarshi sai yaga mata cikin rauni ta galaba a kwance. Ya tambayeta abin da ya faru, da jin abin da ya faru, sai tausayin ta ya kama shi, sai ya dauke ta zuwa cikin gurin bautar nan. malamin ya kasance mai kudi ne babba, sai ya dau nauyin maganin ta, ba dadewa sai duk raunukan jikinta suka warke tas.
Dama yana da wani da qarami, sai ya danqa mata shi, tayi masa tarbiya. sannan kuma yana da wani bawa, Shi kuma bawan nan sai ya kamu da son ta, kuma ya buqaci shayar da sha\'awarshi da ita, da barazanar cewa idan bata amsa buqatarshi ba, zai kashe ta. Tace masa zai iya yin duk abin da yaso, amma ita ba zata taba aikata sa6o ba. Sai bawan nan ya kashe yaron nan, sannan yaje ya gayawa malamin yahudun nan cewa, halaccin da ka yiwa matar nan ga abin da ta saka maka dashi (wato kashe Dan ka).
Malamin ya kirawo ta ya tambayeta dangane da kisan danshi, ta gaya mashi gaskiyar abin da ya faru dangane da bawan nan, amma duk da haka, malamin bai yarda da ita ba, yace baza ta cigaba da zama a gurinshi ba, sai ya dauko kudi Dirham 20 ya bata, yace ta kama hanya ta bar mashi guri. Haka matar nan ta bar gurinshi ta dauki hanya, ta shafe dare tana tafiya, har ta isa wani qauye kashegari da safe.
A can ta iske wani mutumi a rataye bai qarasa mutuwa ba, ta tambayi mutumin nan da yake a bakin mutuwa dalilin haka, yace Mata kudi ake binshi har kimanin Dirhami 20, Su kuma a al\'adar garin idan bashin da ake bin mutun ya kai Dirhami 20, to Ana zuwa a rataye mutun ne har sai ya biya ko an biya masa, ko ya mutu haka, da jin haka, sai ta bashi wannan kudin nata Dirhami 20, tace ya biya, sai aka kwanceshi aka sake shi, sai mutumin yace: lallai wannan Mata mai karimci kin ceci raina daga mutuwa.
Dan haka na za6i in kasance tare dake a matsayin mai hidima a gareki. Suna tafiya sai suka isa bakin teku inda suka ga jiragen ruwa, sai mutumin ya cewa matar jira a nan ina zuwa, zan je inyi wa masu jirgi aiki, domin in samo mana abin da zamu ci abinci, sai ya je gurin masu jirgi, ya tambaye su, wacce irin hajja ce (kaya) dasu a cikin jiragen su? Suka ce masa a daya jirgin kayan yari da awarwaro ne masu qima Shi kuma dayan shine Wanda suke hawa wajen tafiye-tafiyen su, sai yace musu zasu kai nawa qimar kayayyakin ku, sai suka ce, gaskiya baza mu iya sanin qimarsu ba duka saboda darajarsu, sai mutumin yace musu, ina da abun da yafi kayan nan naku qima, suka ce menene haka? Yace musu Wata kyakkyawar baiwa ce yarinya, mai kyawun da baku ta6a ganin irinta ba. Sai suka buqaci ya sayar musu da ita, sai yace amma da farko sai dayan ku yaje ya ganta, amma ta yanayin da baza ta fahimci cewa ita aka je gani ba, sannan sai azo a biya ni kudina.
Sannan kuma idan na tafi sai kuje ku dauki abarku, sai suka yarda da haka, sai dayansu yaje ya gano ta, ya dawo ya gayawa \'yan uwanshi cewa, ai kuwa tayi kuma bai ta6a ganin mace mai kyawu irin ta ba. Sai wannan maci amanar mutun ya sayar musu da ita akan kudi Dirhami dubu goma (10,000) ya karbi kudin ya gudu abinshi. Da ya 6ace, sai suka je gurinta suka ce, ke yarinya baiwa, tashi ki shiga jirgi mu tafi, tace Dan me? Suka ce, mun saye ki daga ubangijinki, sai tace ai ba shine mamallakina ba, ni ba baiwa bace. suka ce, kada ki kawo mana wani wargi, kawai kizo mu tafi, in ba haka zamu dauke ki ta qarfi.
Dan haka sai ta bisu zuwa bakin ruwa. koda akaje hawan jirgi, sai duk suka rika kishi akan ta, kowa yana tunanin yadda zata zama mallakinshi, sakamakon haka, sai suka qi yarda da juna, sai suka yanke shawarar dora ta a jirgin kayan yarin nan ita kadai, su kuma dukkan su suka hau daya jirgin.
A yayin da jiragen suka isa tsakiyar ruwa, sai Allah Ya aiko da iska mai qarfi, ta kifar da jirgin da suke ciki, duk suka nutse. Shi kuma jirgin da matar take ciki, sai iska ta kaishi wani tsibiri, da ita da kayan a ciki. A can ta ga wani gida mai kyawu, ga Wata qorama kusa dashi, da bishiyoyi masu kayan marmari masu kyau a kewayen sa. tace a ranta anan zata zauna ta qarasa rayuwarta, tana bautawa Allah tana ci daga wadannan \'ya\'yan itatuwa ta sha daga ruwan qoramar nan mai kyau har qarshen rayuwarta. Sai Allah Ya yiwa daya daga cikin annabawa na wancan lokacin wahayi, cewa yaje ga sarkin nan (mai wancan alqalin na farko), ya sanar dashi cewa, a tsibiri kaza... akwai wata yarinya mumina, ya debi duk mutanenshi suje su same ta, suyi iqrarin laifukansu da suka yi a baya, sannan su nemi yafiyarta, idan ta yafe musu, sannan Ni kuma zan gafarta musu, idan ba haka ba, to Zan saukar musu da azaba mai radadi. Da samun wannan umarni daga Annabin Allah, sai sarkin nan ya hada al\'umma suka tafi tsibirin nan, suka iske matar nan a can.
Sai sarkin ya fara matsawa kusa da ita, cikin girmamawa, yace, wannan Alqalin ya gabatar min da matar Dan uwanshi, yace ta yi zina, ni kuma ba tare da qwaqqwaran bincike ba, kuma ba tare da kirawo sahihan shaidu ba, nasa aje a jefe ta, dan haka ina tsoro cewa nayi hukumci ba bisa adalci ba, ki roqa min Allah Ya gafarta min, sai tace zauna nan, Allah zai gafarta maka. Sai kuma mijin ta ya matso gabanta (ita kuma ta shaida shi) sai yace, ina da Mata mumina. sai sarki ya aika ni domin wani aiki a wani gari, duk da yake bamu so tafiyar ba, sai na barwa Dan\'uwana alqali amanar ta, to dana dawo sai Dan uwan nawa ya gaya min cewa tayi zina, an jefe ta, to shine nake jin tsoron ko ina da laifi a wannan alamari, dan haka ina neman ki nema min gafara a gurin Allah.
Kaima Allah Ya gafarta maka, zauna nan, ta zaunar dashi kusa da sarki. Sannan sai alqali shima yazo ya gafatar da laifin da yayi kuma ya nemi tayi masa addu\'a akan laifinshi, shima tace ya zauna anan Allah Zai gafarta masa. Sai kuma wannan faada (malamin yahudu) din shima yazo ya fadi nashi alamarin, shima tace dashi ya zauna anan, Allah Zai gafatar mashi. Daga shi kuma sai bawanshi, shima yazo ya gafatar da mummunan aikin da zaluncin da yayi, ya nemi tayi masa addu\'a ko ya sami rabauta, tace shima ya zauna anan, Allah Yai maka gafara. Sai mutun na qarshe wannan mutumin da ta ceta sakamakom bashi, da aka daureshi, shima yazo ya gafatar da mummunan aikinshi, kuma ya nemi tayi mishi addu\'a dangane da rashin godiyar da ya nuna.
Daga nan sai muminar matar nan ta dubi mijinta tace masa, nice matarka, kuma duk abin da kaji dinnan, to nice duk hakan ya faru akai na. Kuma yanzu ni bani da sha\'awar ko buqatar miji ina so ka dauki wannan jirgin dake cike da kayan yari, kaje dashi domin buqatuwarka, ni kuma ka barni anan in qarasa rayuwata wajen bautar Allah kawai, kaga dai yadda na wahala a hannun mutane. Ya yarda da haka, ya dauki kayan nan tare da sarki da suaran mutanen gari suka dawo cikin gari abinsu.
MUHIMMANCIN MAHAIFIYA YA WUCE WASA
An ta6a yin wani bawan Allah mai yawan bautar Allah mai suna Juraih. Ya kasance kodayaushe a daki yana bautar Allah ba dare ba rana. Wata rana sai mahaifiyarshi tazo qofar dakin da yake ibada, yayi kira, amma sai bai amsa mata ba, duk da yaji kiran. Sai ta tafi, daga baya ta kuma dawowa ta kirashi, bai dai amsa Mata ba, har karo na uku tazo ta sake kiran shi, wannan lokacin ma bai amsa Mata ba. Sai ranta ya 6aci, a qarshe dai sai tace: "ina roqon Allah da kada Ya taimakeka."
kashegari sai ga wata Mata dauke da cikin shege, tazo gurinshi, cikin ciwon naquda, sai ta haihu a nan dakin nashi, kuma taje ta watsa labari cewa, Dan na Juraih mai ibada ne. Sai labari ya watsu a gari, sai duk gari aka dauka Ana cewa, oh!! mutumin da kullum yake hantarar (suka) mazinata, ashe shima shine!. Sai sarki yasa a kashe Shi, jin haka sai mahaifiyar tashi, ta rugo a guje zuwa gareshi tana yin kuka. Sai Juraih yace: ya Ummi! kukan me kike yi yanzu? kiyi shiru kawai, ke kika jawo min wannan bala\'in ta hanyar bakin ki. da mutane suka ji wannan tattaunawar sai suka tambayi, me ya faru, bayan Juraih ya gaya musu duk abin da ya faru, sai suka ce, to ta yaya zamu iya gamsuwa da duk abin da ka gaya mana?
sai Juraih yace ku kawo min Shi jaririn, da kanshi zai fadi gaskiya. Sai aka kawo mashi jaririn. Juraih ya dauki jaririn ya rungumeshi, sannan yayi addu\'a, sai ya tambayi jaririn: Waye mahaifinka? sai yaro ya fara magana da iznin Allah cewa: makiyayi wane... na guri kaza, qabila kaza! shine mahaifina. A taqaice dai Allah Ya \'yantar da Juraih daga kisa. Tun daga rannan Juraih yayi rantsuwa da kuma qudurin cewa bazai qara yin nisa da mahaifiyarshi ba kuma zai kasance kodayaushe cikin hidimta mata.
INGANTACCIYAR LAFIYA ITACE SAMUN ZUCIYA MAI KARBAR GASKIYA
Wata rana Annabi Isa (alaihissalam) ya je wucewa ta wani guri sai ya ga wani mutum da aka jarabceshi da cututtuka iri-iri: babu idon da zai gani, babu qafa ga kuma rashin lafiyar Fata. to a daidai lokacin da Isa (alaihissalam) yazo kusa dashi, mutumin yana Jan jiki yana tafiya, sai ya fada rami (kwazazzabon kan hanya), sai mutumin nan yace "Godiya ga Allah da ya bani lafia kuma Ya sani cikin salama," da Annabi Isa yaji shi, sai yace mashi "kai kuwa bawan Allah me yayi saura daga cikin bala\'o\'in da ba a saukar maka ba, har kake godiyar lafia haka?" sai mutumin yace "Lafiya da Salama ta sun fi na mutumin da ZUCIYAR SHI TA GAZA FAHIMTAR GASKIYA DA KUMA KARBAR TA".
Sai Annabi Isa (alaihissalam) yace: "lallai ka fadi gaskiya" sai ya shafa jikinshi, take mutumin ya warke daga dukkan cututtukan nashi, da iznin Allah. Haka ya ci gaba da rayuwa cikin biyayya ga umarnin Allah har ya koma ga Allah. Allah Subhanah Ya azurtamu da shaida gaskiya da kuma karbarta, a duk inda take. Ameen ya Rabbi.
NEMAN HALAL YANA DAGA BABBAR IBADA
wata rana Annab Isa (alaihissalam) ya je wucewa ta wani guri, sai ya iske wani ya ke6e guri yana ta bautar Allah, sai Isa (Alaihissalam), ya tambaye Shi, "me kake yi anan?" sai ya amsa masa cewa "Bauta (ibada)" sai Annabi Isa yace mashi to a ina kake samun abinci da abin sha? sai yace, "ina da wani dan uwa da yake samowa ya kawo min." sai Annabi Isa (alaihissalam) yace "to Shi dan\'uwan naka, shine mafificin mai ibada akan ka."
KIN BIYA MUMMUNA DA KYAKKYAWA:
Wani yaro Dan primary wata rana da yamma, yaje ya sami maman shi a dakin girki tana yi musu miyar abincin dare, sai ya miqa mata takarda wadda take dauke da rubutu, sai ta goge hannun ta a jikin Apron (rigar girki), ta karbi takardar. Ta duba takarda sai taga ya rubuta kamar haka: *** yanke ciyawa = N200
*** share dakina wannan satin = N100
*** zuwa kanti yo miki siyayya = N50
*** tsare miki qane na, kije da kanki = N25
*** fitar da shara waje = N100
*** yin qoqari a makaranta Dan kawo miki good report card = N300
*** sharar tsakar gida = N200. Dan haka total ina binki N975.
Ko!!! Maman tashi ta kalle shi tana tsaye, sai ta shiga tunani, Shi kuma ya qura mata Ido. Sai itama ta dauki abin rubutu ta juya bayan takardar ta rubuta kamar haka:
*** na dauke ka tsawon wata 9, haka ka girma a cikina = Kyauta, bana buqatar komai
*** duk dararen Dana zauna da kai ina rainonka, kuma ina yi maka addu\'a = Kyauta, ban buqatar komai
*** duk jarabawar Dana fuskanta da hawayen da na zubar a tsawon shekaru, duk domin ka = Kyauta, bana buqatar komai
*** tsawon darare ina matuqar firgita da dimauta sakamakon tunanin irin damuwar da zaka iya fuskanta a rayuwar ka nan gaba = Kyauta, bana buqatar komai
*** sama maka kayan wasa (toys), kaya (tufafi), kai hatta ma share maka hanci = duk Kyauta, bana buqatar komai
*** a qarshe idan ka tara duk wadannan, to ka hada da qimar son da nake yi maka = total Kyauta, bana buqatar komai.
a yayin da yaron ya gama karanta abin da maman tashi ta rubuta, sai ga wasu manya-manyan hawaye daga idanun shi, ya kalli maman tashi yace "Mama tabbas ina matuqar son ki." sai ya dauki abin rubutu, ya rubuta da Gwara-gwaran baqaqe:
"PAID IN FULL"