Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

Gajerun labarai masu dauke da darusa

2016/03/04

Gajerun labarai masu dauke da darusa

AJIN AKHLAQ

     KOWA ANA YI MASA JARABAWA A FAGENSHI NE

An taba yin wani malamin Akhlaq (koyar da kyawawan dabi'u) babban gaske, domin yana da dalibai sama da dubu da suke sauraren darussan shi na akhlaq kuma suna anfanuwa. Amma saidai Kash!!! shi kuma sai aka jarabashi da shaidaniyar Mata, domin matar nan tashi, ta kasance mai tsananin Tsiwa da Bala'i, kuma kullum al'amarin sai gaba, shi yasa ma wannan malamin kullum idan dalibanshi sunzo gaishe shi kafin a fara karatu, sai ya rika qoqarin saurin fita saboda kada su fahimci halin da yake ciki, to amma yau da gobe taki wasa, sai da daliban suka lura da abin da yake qoqarin boye musu. sai wata rana wani daga cikin daliban yake cewa malamin, "Allah Ya gafarta malam, ya kake azabtuwa haka ai ina ganin da ka sawwaqe mata, ai sai ka huta"!!! Sai malamin yake ce masa "Hakane amma idan nayi haka, wato idan na sake ta, to cikin biyu za ayi daya: ko taje ta auri wani shima ya dandana wannan azabar da nake sha, ko kuma taqi auruwa ta shiga cikin wani hali na matsi da takura, NI KUMA DUKAN BIYUN NE BANA SO, shi yasa a gurina yafi in cigaba da jure halinta, tunda ni saba ma, saboda kada cutarwarta ta isa ga wani koda kuwa gareta ne."

*****                                    

 

    SAHIHIN TUBA

wata rana Imam Musa alkazim Alaihissalam zai wuce ta qofar gidan wani mai kudi shagalalle mai suna Bishr Hafiy a garin Baghdad. sai Imam yaji kide-kide da hayaniyar alamun rawa, a gidan wannan mutumin, daidai lokacin da Imam ya iso saitin qofar gidan, sai ga wata mai kidimar gidan ta fito domin zubar da shara, sai Imam ya tambayeta kamar haka: "ya ke baiwar Allah shin mai gidan nan '...yantacce ne, ko kuwa Bawa ne?." sai tace: "'yantacce ne". sai Imam yace: "lallai kin fadi gaskiya, Dan da Bawa ne, to da yaji tsoron ubangijin shi." shikenan sai ta koma gida abinta, da ta shiga sai ta iske Bishr a gaban shimfidar liyafa (abinci iri-iri) ga giya nan kala-kala, sai yake tambayarta dalilin dadewarta, sai ta gaya mashi ga Wanda ya tsayar da ita kuma ga abin da ya gaya mata. jin wannan magana ta ma'asumi, sai tayi masa tasiri, sai daga gindin shimfidar nan, qafar Shi ko takalmi babu wato HAFIYAN, sai ya fito waje a dimauce, yabi inda Imam ya nufa, har ya tarar dashi, yana mai yin KUKA, NADAMA da NEMAN UZIRI, akan sabon da yakeyi, a qarshe dai ya karbi tuba a hannun Imam. Tun daga lokacin, sai ya shagaltu da yiwa Allah biyayya, ya zama Zahidi kuma A'rifi, har qarshen rayuwar shi, Dan ya ma kasance cikin manya-manyan A'rifai na Qarni na Uku. Allah ka gafarta mana kuma Kasa mu dace da Tuba sahihi.

   

SAKAMAKON CEWA 'ALHAMD'LILLAH' SAI DA YAYI ISTIGFARI NA TSAWON SHEKARU 30

Abul Hasan Sara Saqati yana daga cikin A'rifan Qarni na uku, ya kasance kuma Dan kasuwa, wato yana da shago a Wata kasuwar garin Baghadada (Iraqi), sai Wata rana da dare wuta (gobara) ta kama a wannan kasuwar da shagonshi yake, sai ya fito cikin hanzari ya nufi kasuwar, sai ya hadu da wani a hanya, sai mutumin yake gaya mashi, shagonka bai qone ba. jin haka sai yace 'Alhamd'lillah', yana fadar haka kuma sai ya farga cewa, shagunan mutane fa sun qone, Amma Shi yace alhamdlillah saboda ban da nashi! ai tun daga wannan lokaci ya fara ISTIGFARI akan fadar Alhamdlillah sai da yayi shekaru Talatin (30) yana yi.

 

 

    YA MAI SUTURCE AIBUKA

An taba yin fari (qarancin ruwa) a wani gari a Iraqi a zamanin da can. wadda mutanen yankin suka yi ta roqon ruwa Amma ba sami ijaba (amsawa) ba, sunyi addu'o'in roqon ruwa ba 1 ba, ba 2 ba, amma ba a dace ba, suka fito da yara da dabbobi suna kuka, amma duk ba a dace ba. Akwai wani malami bawan Allah qwarai, har da shi a addu'o'in amma, ba labari. sai malamin nan ya koma... dakin shi yana ta kuka yana yabon Allah da harshen bayin Allah ma'asumai. ana haka bayan sallah, ya Dan kwanta sai yayi mafarki da wani bawan Allah mai tsarki, ya gaya masa cewa: suje qauye kaza... akwai wani makiyayi acan mai suna kaza, su same shi, suce ance ya roqa musu ruwan sama. sai ya tashi, sai yaga ai mafarki ne, sai ya koma baccinsa, sai ya kuma ganin hakan a mafarkin, ya kuma komawa baccin sa, har dai sau uku, a qarshe dai ya tashi ya sanar da wasu manyan mutanen garin, sai suka zabi wasu kadan daga cikin su, suka nufi waccan qauye da aka yiwa malamin nan ishara dashi. da suka isa qauyen, suka sami mutumin nan, ya fito da dabbobinshi zai tafi kiwo, suka tsayar dashi suka ce yayi musu addu'ar samin ruwa, yace: shi a wa? suka dai takura shi, sai yace to, ni dai nasan ba kowa bane ni, Amma tunda kun takura, bari inyi, sai ya daga hannunshi yayi musu addu'a ga Allah subhanahu wa Ta'ala, sauke hannunshi ke da wuya, sai hadari ya fara haduwa, sai ga ruwa, har mutanen nan suka jiqe, kafin su Sami mafaka. to anyi haka, sai kuma mutanen nan suka dame Shi da cewa, Dan Allah ya gaya musu, me yake yi haka, har ya taka wannan matsayi babba? yace kai mutanennan kun ganni dai kiwo zan tafi kuka tare ni ko, to ni dai daga kiwon nan ba abin da nake yi, sai wajuba da suka hau kaina nake qoqarin saukewa, Dan hatta ko nafila bana samun yi, saboda shagaltuwa da kiwona. suka dai takura shi, suka ce sudai basu gamsu ba, kodai ya boye musu wani abu. A qarshe dai yace, to, Shi dai abin zai iya gaya musu kenan, sai kuma wani abu daya da zai iya tunawa dashi, wadda yana ganin ba wani abu bane babba. Abun kuwa shine: Matata ta farko wadda ta rasu, lokacin na ya aure ta, koda aka kawota, tun daga daren farko sai tayi ta yin kuka ta kunshe a kusurwar daki tana ta kuka, nayi ta rarrashinta, ina cewa 'ba gani ba ai na isheki dauke kewa, inma kina ganin har yanzu baki shirya rabuwa da gidan ku ba, to ki koma ki zauna tare da iyayen ki, ni sai in rika zuwa gurinki', nayi-nayi dai in rarrasheta amma taqi daina kukan, a qarshe dai tace: duk abin da kake fadi ba sune matsala taba, matsala shine: "Nazo gidan ka ne da ciki Wata 3, kuma kasan idan iyayena suka ji kasheni za su yi kamar yadda ka sani a al'adarmu". hakan yasa na boye maka, kuma yanzu bansan yadda zanyi ba. sai nace Mata indai wannan ne tayi shiru, nayi Mata alqawari muddun tana raye babu Wanda zai sani, kawai ta tubarwa Allah, ni kuma zan cigaba da zama da ita a mata ta, da kulawa, har ta haihu, kuma zan riki dan kamar nawa, kuma bana so ta gayawa koda yaron/yarinyar da zata haifa cewa ni ba ubanshi/ta bane. Haka muka yi, kai saboda kada mutanen garin su fahimci wani abu misali suga ta haihu da wuri, sai na sa ta hada mana kayan mu mu bar garin, sai na gayawa makusanta na cewa zamu je wani gari ci' rani, Dan haka a yafe mu, sai sun ganmu. haka muka bar garin nan, muka tafi can wani garin da ba a San mu ba. ta haihu a can, har yaro yayi wayo. bayan 'yan shekaru muka dawo. ba dadewa da dawowar mu, Allah Yayiwa yaron rasuwa. To kunji abin da nasan nayi, kuma nima ina roqon ku, iya ku dinnan, da kubar wannan abu a ranku, kar ku gayawa kowa, har sai bayan na koma ga ubangiji na. Allah ka dada suturce mana aibukanmu, Ameen.

 

     AIKIN ALKHAIRI BAYA GUSHEWA HAKA

An taba yin wani mutumi mai arziqi da ya rika yiwa mabuqata hidima da dukiyarshi, bayan Allah Yayi masa rasuwa, sai matar sa ta cigaba da yiwa mabuqata hidima da dukiyar da ya bari. to mutumin ya bar Da qarami, bayan da yaro yayi girma, ya fara fita sai ya zamana duk inda yaron nan yaje a garin nasu sai mutane suyi ta sa masa albarka, suna yiwa mahaifinshi addu'ar ...alkhairi da Rahma. Sai wata rana yaron nan bayan ya zama saurayi, yake tambayar mahaifiyarshi, wai meye dalilin da yasa duk inda naje sai mutane suyi ta yi min addu'a tare da mahaifina?, sai mahaifiyar tashi tace masa: Mahaifinka ya kasance mumini mai tsoron Allah, kuma Allah Yayi mashi arziqi, amma sai ya rika yin hidima wa mabuqata da dukiyar tashi, ni kuma da ya rasu, sai na cigaba da hakan, har na qarar da dukiyar. Sai yaron yace ya abin sona (mahaifiyata)! marigayi mahaifina ya samu lada dangane da wancan aiki mai kyau da yayi da dukiyarshi, amma ke baki da ikon yin abin da kika yi da ita, dan haka ke saidai ki sami fushin Allah da abin da kika yi. sai mahaifiyar ta tambayeshi , me kake nufi da haka Dana? Sai Dan yace, mahaifina ya bayar da dukiyarshi ne, amma ke dukiyar wani kika bayar (wato nufinshi dukiyarshi 'Dan'). Sai mahaifiyar tace gaskiya ne Dana!. amma nayi tunanin cewa ne baza ka damu ba da hakan, wato na dauka zaka amince da abin da nayi ne, wato na dauka zaka halatta min dukiyar ka ne. Sai Dan yace nayi hakan yanzu, wato na halatta miki abin da kika yi da dukiyar tawa, to Yanzu akwai saura ne? in yaso sai inyi jari da su ko Allah zai sa musu albarka sai kiga muma munyi arziqin! sai tace ina da 'Dinar dari', sai Dan yace, in Allah Yayi musu albarka sai kiga sun yawaita. sai ya karba ya fita domin nema da wadannan kudi a matsayin jari. A kan hanyarshi ta fita zuwa nema, sai ya iske wata gawa ta wani mutun da yaga alamu a fuskar shi, alama ta mumini. Sai yayi tunanin amfani da kudin nan nashi na jari, domin shirya gawar nan da yi mata sutura har zuwa sallah da bisnewa, haka kuwa yayi, wadda a qarshe, yaga saura Dirham 20 suka yi saura a hannunshi, sai yace Allah Yayiwa wadannan albarka. sai ya qara gaba abinshi. yana cigaba sai ya hadu da wani mutun, mutumin ya tambaye shi, Ina zuwa, yaro yace zanje neman halal da albarkar Allah. sai ya tambaye nawa ne yake dasu a matsayin jari? yaro yace masa Dirham 20, sai mutumin yace, Me 'yan wadannan kudin zasu yi maka a matsayin jari?, sai yaron yace, Idan Allah Yayi musu albarka, sai kaga sun yawaita. sai mutumin yace haka ne yaro ka fadi gaskiya. To amma ina so kayi duk abin da zance maka, amma da sharadi daya, sharadin kuwa shine, Duk abin da ka samu, to zamu raba shi daidai. Yaro ya yarda da haka. Sai mutumin ya gaya mashi, Akan wannan hanyar da zaka bi zaka iske wani gida a gaban ka, mai gidan zai gayyace ka baqunta zuwa gidanshi, to ka amsa gayyatarshi, kuma a yayin da mai hidimar gidan zai kawo muku abinci, zaizo tare da wata mage baqa a hannunshi, to ka tambayeshi ya siyar maka da ita, zai qi da farko amma ka takura, a qarshe zai yarda ya sayar maka da ita akan Dirhami 20 (wato duka kudinnan naka), to lallai ka biya hakan, ka karbi magen. daga nan sai ka yanka magen ka qona ta, sai ka cire qwaqwalwarta ka kulle a wani abun sai ka cigaba, zaka isa wani Birni

idan ka kulle tokar qwaqwalwar magen nan a cikin qyalle ko wani abin, sai ka cigaba zuwa wani birni. Zaka samu sarkin garin ya makance. Ka gayawa mutanenshi cewa zaka yi mashi magani. Kada ka tsorata da ganin gawawwakin wadanda sarkin yasa aka kashe sakamakon gazawa wajen yi mashi magani. Zaka iya sanya duk farashin da kake buqata na kudin maganin da zaka yi mashi. A ranar farko sai kayi amfani da Mishi (tsinken sa kwalli), sai ka dangwali wannan tokar qwaqwalwar magen, sai ka sa a idon sarkin kamar kwalli, zai fara jin sauki, kuma zai buqaci da yawa, to kada ka bashi, kawai ka kuma sanya mashi da mishin nan kamar na farko, a rana ta uku ma kayi haka, zai warke duka. shikenan Yaro ya tafi ya fara isa gidan farko, ya sayi mage (kyanwa), yayi duk abin da aka gaya mashi, ya nufi wancan birni, ya iske sarki, ya fara magani kamar yadda aka umarce shi. Tun a rana ta farko da ya sanyawa sarki magani, sarki ya fara jin sauki, zuwa rana uku, sarki ya warke tas, ganin shi ya dawo kamar baiyi makaranta ba. Sarki ya rungume yaro yace, kayi min babban taimako, yanzu saura nine zan saka maka. ka dawo min da masarauta ta gareni. sakamakon haka na baka 'yata a matsayin mata, na aura maka ita. Sai yaron yace, Mahaifiyata tana raye kuma bazan iya rabuwa da ita ba. Sarki ya aura masa ita, kuma yace, zaka iya zama har iya rayuwarka a wannan masarauta, kuma in kana so zaka iya komawa wajen mahaifiyar ka, tare da matar ka (wato Gimbiya). sai yaro ya zauna har tsawon shekara daya tare da sarki cikin girmamawa da karimci, sannan ya fari shirye-shiryen tafiya. Sarki ya bashi: dukiya, kaya, raquma, shanu da tumaki masu yawa. yaro ya hada duka kaya tare da matarsa ya sau hanya, sai ya biya ta gurin mutumin da ya gaya masa yadda ya warkar da sarki. ya sami mutumin a gurin kuwa. da ganin yaron kuwa mutumin yace, kai yaro ya baka cika alqawari ba? sai yaro yace, da farko ina roqon ka da ka shafe min abubuwan da nayi amfani dasu a yayin da na zauna acan gurin sarkin tsawon shekara. sannan kuma duk wani abu da na samo ga su nan tare dani, sai ka dauki Rabin su. yaro ya raba dukkan dukiya biyu, yace mutumin ya zaba. sai mutumin yace, yaro baka yi adalci ba. Yaro yace kamar yaya fa? Sai mutumin yace wannan matar ma tana cikin abubuwan da ka samo. yaro yace hakane kana da gaskiya. Dan haka, ka dauki dukkan dukiyar, sai ka bar min Matar. sai mutumin yace, a'a! itama Rabin ta nake buqata. sai yaro ya buqaci Zarto, ya dora a kan ta zai raba ya bashi, sai mutumin yace: Yanzu ka cika alqawari da kuma maganarka. wannan matar da dukkan dukiyar nan ka rike sun zama naka. ka tafi da kayanka, bana buqatar komai daga ciki. Ni dama Mala'ika ne, Allah Ya aiko ni, in baka Lada daga cikin ladan aikin alkhairin da kayi ga Gawar nan da ka iske a hanya lokacin da ka fito daga garinku.