Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

Dan agajin tsuntsu

2016/03/06

Dan agajin tsuntsu

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin qai

 

Dan kwana-kwanan (dan agajin) Tsuntsu

(tsuntsun da ya kawo daukin kashe wuta)

Duk lokacin da wuta ta tashi a wani guri a doron qasa, sai kaga Rahamar Allah ta kawo dauki a gurin, wato ba ta zura ido tana gani a sakamakon makirci da hassadar azzalumai, jikuna da gidajen waxanda ba su ji ba kuma ba su gani ba, su zama toka.

Wani Sufi yana hakaito qissar wani tsuntsu xan kwana-kwana (xan agaji), inda yake cewa: tsuntsun domin kashe babbar wutar da azzalumai suka shirya wa Annabi Ibrahim (AS), sai ya riqa xauko xigo-xigo na ruwa a bakinsa yana zuwa saman harshen wutar nan yana xigawa.

Sai aka ce dashi:

Waxannan xige-xigen ruwa ta yaya za su iya kashe wannan babbar wuta haka?

Sai tsuntsun ya ba su amsa kamar haka:

Na sani cewa ba za su iya kashewa ba, amma a lokacin da zalumci ya rufto akan masoyin Allah (Khalilul-lah), sai mutane suka kasu gida biyu, vangare xaya masu laifi wato masu qetare iyaka da kuma xayan vangaren sune Adilai kuma 'yan amana wato masu cika alqawari.

To nima da wannan aikin ne nake son nuna tabbatuwa ta tare da vangaren da yake akan daidai da kuma nuna barranta (nisanta) ta daga waxanda suka kunna wutar, haka kuma ga waxanda suka yarda da aikinsu kuma suka qarfafa su akai.

Addinin musulunci a mahangar Shi'a Imamiyya, kodayaushe ta hanyar hikima da zaburarwa ta hanyar maganganu da ayyukan Tsarkaka (Alaihim-al-salam) yake kira, kuma ta hanyar tabbatuwa akan alqawari da cika umarninsa yake kira ga fito-na-fito da zalumci da munanan xabi'u da kuma hankula ko tunane-tunanen da suka kaucewa hanyar gaskiya.

Kamar yadda alqur'ani mai tsarki ya tabbatar, yin wa'azi ko nasiha mai kyau, biyayya da tsarkakewa, ya zama wajibi a kiyaye waxannan sharuda kamar haka:

  1. Dole ne niyyar mutum tun daga fara aiki har zuwa qarenshi, ta kasance tsarkakakka kuma domin Allah Maxaukakin Sarki.
  1. Dole ne tunane-tunane da fikirori su kasance a bisa ginshiqai bayyanannu, daidaitattu kuma nagartattu.
  2. Haka kuma dole ne abubuwa da hanyoyin da za a yi amfani da su wajen aiwatar da wannan al'amari, su kasance a samar da su ta hanyar da ta dace kuma a yi amfani da su ta hanyar da ta dace, haka zalika dole hadafin abun da za ayi ya zamo tsarkakakke kuma domin Allah ta yadda zai kyakkyawar isa ga zuciya da qwaqwalwar xan adam.