Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Aqida

SALAFIYYA DA TSAYUWAR IMAM HUSAIN A.S.

2016/03/10

SALAFIYYA DA TSAYUWAR IMAM HUSAIN A.S.

بسم الله الرحمن الرحیم

اللهم صلی علی محمد و آل محمد

 

SALAFIYYAH DA TSAYUWAR IMAM HUSAINI (A.S).

ABIN DA YASA NA ZABI WANNAN MAUDHU'IN.

Bincike akan tsayuwar Imam Husain ( a.s ) yana da mahimmanci sosan gaske a fikril islami, wannan kuwa ta hanyar yin la'akari da tasirin da yake dashi a gurin banbancewa tsakanin musuluncin Manzon Allah ( s.a.w.a ) ( Al islam ul Muhammadi Al asiil ) da kuma musuluncin sarakuna (Al islam ul umawiy ), wakazalika da ta hanyar mahimmantarwa da kuma riqo da sunnar Manzon Allah ( s.a.w.a ) wanda ayar Alqur'ni take kiran mu zuwa gare shi: « وَ ما آتاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَ ما نَهاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا » Saboda Manzon Allah (s.a.w.a) ya mahimmantar da wannan tsayuwar kuma har ya zubar da hawaye mai yawa akanta. Wannan ne yasa ni na zabi wannan maudhu'in.

Amma maganar cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya mahimmantar da tsayuwar Imam husain (a.s) kuma har ya zubar da hawaye mai yawan gaske akan ta ba wai da'awa nake yi wacce babu dalili ba, bal wannan haqiqa ce tabbatatta a gurin malaman musulmi – sunna, salafiya, shi'a … Saboda cire shakka bari mu naqalto wasu daga cikin abinda suka ruwaito a cikin littafan hadisan su:

ABU YA'ALA:

عن عبد الله بن نجي عن أبيه : أنه سار مع علي وكان صاحب مِطْهَرَته فلما حاذى نينوى وهو منطلق إلى صفين فنادى علي :

إصبر أبا عبد الله إصبر أبا عبد الله بشط الفرات، قلت : وماذا يا

أبا عبد الله ؟ قال : دخلت على النبي ( ص ( ذات يوم و عيناه تفيضان، قال : قلت يا نبي الله أغضبک أحد ؟ ما شأن عينيک

تفيضان ؟ قال : بل قام جبريل قبل فحدثني أن الحسين يقتل بشط

الفرات، قال : فقال : هل أن أشمک من ترابه ؟ قال : قلت : نعم، قال : فمد يده فقبض قبضة من تراب فأعطانيها فلم أملک

عيني أن فاضتا .

Daga Abdullah dan naji daga babansa: haqiqa yayi tafiya tare da Ali kuma ya kasance mai kula da abin tsarkinsa, a lokacin da Ali yaje Nainawa a hanyar shi ta zuwa siffin sai yayi kira da cewa: kayi haquri Aba Abdullah, kayi haquri Aba Abdullah da bangaren (yankin) furat, sai nace: me zai faru ga Aba Abdullah? Sai Ali yace: wata rana Na shiga gurin Annabi (s.a.w.a) sai Na ga idanun shi suna zubar da hawaye na tayar da hankali, sai nace ya Annabin Allah wani ya fusata ka ne? me ya sami idanun ka suke zubar da hawaye sosan gaske haka? Sai Manzon Allah (s.a.w.a) yace: dazu jibrilu ya bar nan, ya bani labari cewa za a kashe Husain a bangaren furat, sai yace: in shinshinar da kai qasar da za a kashe shi akai? Sai nace: eh, sai ya miqa hannun sa ya danqo danqi daya daga qasar, sai ya bani, Saboda haka na kasa mallakar idanu na har suka zubar da hawaye sosan gaske.

Wanda yayi tahaqiqin littafin Sheikh Husain Salim Asad yayi qarin haske da cewa: WANNAN HADISIN HASANUN NE. (a duba Musnadu Abi ya'ala, tahaqiqin Husain salim asad, Bugun Dimashq: darul ma'amun litturath, Bugun farko 1404a.h (1984), juzu'i na 1, shafi na 298, hadisi na 363).

AL HAFIZ UL HAITHAMI Shima ya fitar da wannan hadisin a cikin littafin sa, bayan haka sai yace: « رواه أحمد وأبو يعلى والبزار والطبراني ورجاله ثقات ولم ينفرد نجي بهذا » Ahmad, Abu ya'ala, Bazzar, Tabarani duk sun ruwaito shi, kuma wadanda suka zo a cikin isnadin sa SIQOQINE bawai kawai a gurin naji aka ji wannan ba. (A duba Majma'uzzawa'id Wa Manba'ul fawa'id, Bugun Beirut: darul fikr, shekara ta 1412 a.h, juzu'i na 9, shafi na 300, hadisi na 15112.

Wannan kenan sai dai Allamah Albani yayi gyaran fuska da cewa : « وهذا إسناد ضعيف، نجي والد عبد الله لا يدری من هو کما قال الذهبي، و لم يوثقه غير ابن حبان، وابنه أشهر منه فمن

صحح هذا الإسناد فقد وهم .» (Wannan isnadi ne mai rauni, naji mahaifin Abdullah ba a san ko shi waye ba kamar yadda zahbi ya fada, ba wanda yace shi siqa ne in ba ibn hibbaan ba, dan sa yafi shahara a kansa, saboda haka duk wanda ya ingantar da wannan hadisin to haqiqa yayi wahami).

sannan sai ya kawo maganar Alhafizul'haithami na cewa: Ahmad, Abu ya'ala, Bazzar, Tabarani duk sun ruwaito shi, kuma wadanda suka zo a cikin isnadin sa SIQOQINE kuma ba wai kawai a gurin Naji aka ji wannan ba. Sai yace : « قلت : يعني أن له شواهد تقويه و هو كذلك .» (Nace: yana nufin cewa akwai shedun da zasu iya qarfafa hadisin, tabbas kuwa haka ne) sannan sai ya fara bayanin hanyoyin da aka naqalto wannan hadisin wanda ya kawo hanyoyi guda shida sannan sai yace: « قلت : وبالجملة فالحديث المذكور أعلاه و المترجم له صحيح بمجموع هذه الطرق و إن كانت مفرداتها لا تخلو من ضعف و

لكنه ضعف

يسير ، لاسيما و بعضها قد حسنه الهيثمي » (Nace: a taqaice idan akayi la'akari da wadannan hanyoyin hadisin ya inganta, duk da yake wasu kalmominsa suna da rauni saidai dan kadan ne, musammam ma da ya zama Alhaithami ya hasanan tar da wasunsu) «a duba Silsilatul Ahadisis Sahihah Wa shai'un Min Fiqhiha Wa Fawa'idiha, Riyad: Maktabatul Ma'arif Linnashri Wattauzi'i, 1415a.h. (1995), juzu'i na 3, shafi na 159 – 162, hadisi na 1171»

FA'IDA Dan uwa mai karatu a nan Alhafizul'Haithami da Allamah Albani sun baka wata qa'ida a ilmin hadisi a hannu cewa ba a wurgi da hadasi don isnadin sa na da rauni sai idan ba a sami abun da zai qarfafashi a wasu hadisai ba. kokuma muce rashin ingancin isnadin hadisi baya nuna rashin ingancin mataninsa, saboda qa'idar da malaman musulmi suke aiki akan asasin ta a gurin jarhi da ta'adili itace rabawa tsakanin ingancin isnadin hadisi da kuma ingancin mataninsa, saboda ingancin dayan su bai dogara ba akan ingancin daya ba, wato daya zai iya inganta ba tare da daya ya inganta ba. KA KIYAYE WANNAN.

IBNUL HAJAR ALHAITAMI Shima ya fitar da wannan hadisin ta hanyar ibn sa'ad daga sha'abi, saidai akwai wasu abubuwa da suka zo a cikin sa wadanda ba su zo ba a wanda ya gabataba, saboda haka babu laifi mu gabatar ma dan'uwa mai karatu su, kamar haka: -Imam Ali da yajenainawayatsayayatabbayisunangurin, sai aka ce masa KARBALA. « أخرج ابن سعد عن الشعبي قال مر علي ) رضي الله عنه ( بكربلاء عند مسيره إلى صفين وحاذى نينوى قرية على الفرات،

فوقف وسأل عن اسم هذه الأرض، فقيل كربلاء . » « فبكى حتى بل الأرض من دموعه » -Yayi kuka har ya jiqa qasar gurin da hawayensa. -jibirilu ya shunshuna ma Manzon Allah ( s.a.w.a ) qasar sannan yayi kukan. « شمني إياه فلم أملك عيني أن فاضتا » «a duba Assawa'iqul Muhriqa Ala Ahlil'Rafdi Waz'Zandaqa, Tahqiqin Abdurrahman ibn Abdullah Atturki da Kamil Muhammad Alkharat, Bugun Beirut: Muassasatur'risala, bugun farko – 1997, juzu'i 2, shafi na 566.

MUTTAQA AL'HINDI:

« عن المطلب بن عبد الله بن حنطب عن أم سلمة قالت : كان النبي ) صلى الله عليه وسلم ( جالسا ذات يوم في بيتي فقال : لا

يدخلن علي أحد فانتظرت فدخل الحسين فسمعت نشيجالنبي

( صلى الله عليه وسلم ( يبكي، فاطلعت فإذا الحسين في حجره أو إلى جنبه يمسح رأسه وهو يبكي، فقلت : والله ! ما علمت به

حتى دخل، فقال النبي ) صلى الله عليه وسلم ( : إن

جبريل كان معنا في البيت فقال : أتحبه ؟ فقلت : أما من حب الدنيا فنعم، فقال : إن أمتك ستقتل هذا بأرض يقال لها كربلاء،

فتناول جبريل من ترابها فأراه النبي ) صلى الله عليه وسلم )،

فلما أحيط بالحسين حين قتل قال : ما اسم هذه الأرض؟ قالوا : أرض كربلاء، قال : صدق رسول الله ) صلى الله عليه وسلم (،

أرض كرب وبلاء . »

Daga Ummussalamah (r.a.) –matar Annabi– tace: wata rana Annabi (s.a.w.a) Ya kasance zaune a gidana, sai Yace: lalle kar a bari kowa ya shigo gurina, sai na tsaya ina kulawa, sai Husaini Ya shiqa ban da labari, sai naji shasshekar Annabi Yana kuka, a lokacin sai nafahimci cewa Husaini Ya shiga, Annabi Yana rungume dashi ko Yana gefensa Yana shafar masa kansa, sai nace: wallahi ban san lokacin da Ya shigo ba, sai Annabi Yace: lalle jibirulu ya kasance tare damu a wannan dakin, sai yace min: kana sonsa? Sai nace masa: eh, sosai, sai yace: haqiqa al'ummar ka zata kashe shi a wani guri da ake kira KARBALA, sai jibirilu ya kawo min qasar gurin sai ya nuna min. A lokacin da aka kewaye Husaini kafin a kashe shi Yace: meye sunan wanan gurin, sai suka ce KARBALA, sai Yace Manzon Allah Yayi gaskiya, QASAR BAKIN CIKI DA BALA'I. (a duba Kanzul'ummal Fi Sunanil Aqwal Wal Af'al, Tahaqiqin Bakari'hayyani, Mu'assasat'ur Risalah, Bugu na biyar –1401A.h. (1981), Juzu'i na 13, shafi na 656 – 657, hadisi na 37669»

 

ALLAMAH ALBANI: « 677

( عن محمد بن مصعب حدثنا الأوزاعي عن أبي عمارشداد بن عبد الله عن أم الفضل بنت الحارث - 671 / أخرجه الحاكم ) 3

. " أنها دخلت على رسول الله ( صلىالله عليه

وسلم ( ، فقالت : يا رسول الله إني رأيت حلما منكرا الليلة ، قال :و ما هو ؟ قالت : إنه شديد ، قال : و ما هو ؟ قالت رأيت كأن قطعة

من جسدك قطعتو وضعت في حجري ، فقال : رأيت خيرا ، تلد فاطمة إن شاء الله غلاما فيكون فيحجرك ، فولدت فاطمة الحسين ، فكان في حجري كما قال رسول الله ) صلى الله

عليهوسلم ( ، فدخلت يوما إلى رسول الله ) صلى الله

عليه وسلم ( فوضعته في حجره ، ثم حانتمني التفاتة فإذا عينا رسول الله ) صلى الله عليه وسلم ( تهريقان من الدموع، قالت

فقلت : يا نبي الله بأبي أنت و أمي مالك ؟ ... فذکره و قال : صحيح علی شرط الشيخين . وتعقبه الذهبي بقوله : قلت بل منقطع ضعيف،

فإن شداد لم يدرک أم الفضل ومحمد بن مصعب

ضعيف . قلت : لكن له شواهد عديدة تشهد لصحته ...»

Hakim ya fitar daga Muhammad ibn mus'ab Auza'i ya bamu labari daga baban Ammar ibn Abdullah daga ummul fadhli diyar haris cewa ta shiga gurin Manzon Allah (SAWA), sai tace: Ya Manzon Allah nayi mummunan mafarki da dare, sai Yace: me kika gani ne? Tace: bashi da kyau. Yace: me kika gani ne? Tace: naga kamar yankin tsoka a jikin Ka, kuma an ajiye ta a daki na, sai Yace: kinga alkhairi, Fatima zata haifi yaro, insha Allah yaron kuma zai kasance a dakinki. Sai kuwa Fatima (a.s.) ta haifi Husaini (a.s.) kuma ya zauna a daki na kamar yadda Manzon Allah (SAWA) Ya fada. wata rana sai na shiga gurin Manzon Allah (SAWA) na ajiye Husaini a dakin Sa, sannan sai na fahimci cewa idanun Manzon Allah suna zubar da hawaye sosai, sai tace nace: Ya Annabin Allah

fansarka babana da mamata me yafaru?... (Wato sai ya kawo labarin da ya gabata a cikin hadisan da suka gabata) sannan Hakim yace: WANNAN HADISIN SAHIHINE AKAN SHARADIN BUKHARI DA MUSLIM. Sai dai Zahbi yayi masa gyaran fuska da cewa: bal munqada'ine da da'ifi Saboda shaddad baiyi lokaci da ummul fadhli ba, kuma Muhammad mus'ab mai rauni ne. Nace: sai dai yana da shaidu masu yawa da suke shaida akan ingancinsa. (a duba Silsilatul Ahadisis Sahiha, juzu'i na 2, shafi na 464 – 465, hadisi na 821, Zamu wadatu da wannan domin ba muna son mu kawo duk hadisin da yazo a wannan babin ba, kawai muna so ne muyi nuni zuwa ga wannan haqiqar. wannan hadisin yazo a littafan sha'a, zaka iya duba KAMILUZ ZIYARA na Allamah Jafar Muhammad ibn Qulawih, Tahqiqin Amini Abdul husaini, bugun Najaf, Bugun farko – 1357 sh, daga shafi na 55 – 62.

A TAQAICE Idan muka kalli hadisan da suka gabata da makamantansu (kamar ruwayar A'isha, Asma'u, Zainab) da idon basira zamu fahimci cewa Manzon Allah (SAWA) yayi kuka akan Husaini (a.s.), da tsayuwar Sa a gurare daban-daban kamar yadda jibrilu (a.s) ya kawo masa qasar gurin da za a kashe Imam Husaini (a.s) ba sau daya ba. Wannan wani abune da yake a bayyane Saboda hadisin da Imam Ali Yayi bayanin Manzon Allah (SAWA) Yayi kuka ba shi da dangantaka da na bayanin Ummu salma da Ummul fadhli, kamar yadda nasu shima haka bai da dangantaka da na wani, Ummu salma bata san cewa Imam Husaini ya shiga dakin ba, ummul fadhli ita kuma ita taje ta ajiye shi a dakin, wanda fadar Ummu salma ban san Ya shiga ba daliline na cewa ba hadisi daya bane, domin da yakamata tace bansan ta ajiye Shi ba.

ME YASA MANZON ALLAH (SAWA) YAYI KUKA AKAN IMAM HUSAINI (A.S.)? Babu shakka kan cewa Manzon Allah (a.s.) ba yayi tayin wannan koke-koken bane, Saboda Imam Husaini (a.s.) yana jikansa, musammam ma da yazama yayi ta maimaitawa a gurare daban–daban, babban dalili akan haka shine kafa hujjar da Imam Ali (a.s.) yayi da kukan Manzon Allah (SAWA) a lokacin da ya jiqa qasa Saboda kuka a hanyar Sa ta zuwa siffin, ya zaka ce ba haka bane alhali bayan kukan kai tsaye yace: na shiga gurin Manzon Allah na tarar da Shi Yana kuka sosan gaske… kamar yadda ya gabata, wannan yana nuna cewa Imam Ali (a.s.) Yayi kuka ne domin koyi da Manzon Allah (SAWA), wa illa babu buqatar ya fadi cewa Manzon Allah (SAWA) ma Yayi kuka sosan gaske, kamar yadda jibrilu ma ba yayi ta kawo maShi qasar da kuma yi masa Wahayin cewa za a kashe Husaini ba sau daya ba Saboda Imam Husaini (a.s.) kawai yana jikan Sa. Idan an fahimci wannan sai muce: daga cikin abun da yasa – Wallahu Aalim - Manzon Allah (SAWA) Yayi kuka na fitar hankali akan tsayuwar Imam Husaini (a.s.), kuma jibrilu ya kawo qasar da kuma yin Wahayin cewa za a kashe Husaini A.S. ba sau daya ba kawai:

a). Bayanin cewa tsayuwar Imam Husaini (a.s.) tana da mahimmanci da matsayi a addinin musalunci, bal yankine daga cikinsa, wannan kuma Saboda muhimmancin da wahayi da Manzon Allah (SAWA) suka bata. b). Bayanin cewa mustahabbine kuka kan Imam Husaini, wannan kuma Saboda kukan da Manzon Allah (SAWA) yayi tayi a kanSa,

kamar yadda ya tabbata a ilmul Usul cewa idan ma'asumi ya maimaita aiki tor yana Haifar da mustahabbanci, Haza auwalan. Wa saniyan: Saboda koyi da Manzon Allah (SAWA): « لَقَدْ كانَ لَكُمْ في رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كانَ يَرْجُوا اللَّهَ وَ الْيَوْمَ الْآخِرَ » c). Bayanin cewa juyayi akan Imam Husaini (a.s.) bai kebantu da ranar Ashura ba kawai, wannan kuma Saboda kukan Manzon Allah (SAWA) mai tsanani a gurare daban-daban. Dan uwa mai karatu don Allah wanene DAN BIDI'A? wanda ya baiwa tsayuwar Imam Husaini (a.s.) mahimmanci kamar yadda Allah da Manzon Allah (SAWA) Suka bata, kuma yayi kuka kamar yadda Manzon Allah (SAWA) Yayi, ko kuma wanda yake ganin an cika duniya da kuwwa YA HUSAINI YA HUSAINI kuma yake ganin kuka a kanSa bashi da asali a addini. KAYI TUNANI A KAI.

SALAFIYYAH DA TSAYUWAR IMAM HUSAIN (A.S.) KASHI NA 4 Dan uwa mai karatu babu mubalagha idan nace babu wani al'amari da Allah Ya saukar da wahayi a kansa sau da yawa kuma jibrilu idan ya kawo wahayin yakan debo qasar da wannan al'amari zai auku, shi kuma Manzon Allah (SAWA) duk lokacin da aka kawo masa sai Yayi kuka, inba waqi'ar Karbala ba, kamar yadda muka kawo maka wasu daga cikin hadisan da suke nuna haka.

Anan tambaya zata iya zuwa cewa me yasa aka kebance bahasin da daya daga cikin mazhabobin musulunci? me yasa aka sanya SALAFIYYA mihwari (pivot on which this topic revolve) a wannan fagen din? Haqiqa kowa ya sani cewa ma'alasafisshadid lokaci bayan lokaci yakan ji almugalataat'albahitah da almumahikaat'assaqiimah da sokiburutsu wanda wannan ittijahin salafiya ke watsawa kama daga cewa yazidu dan aljanna ne, da kuma cewa bashi da hannu a kashe Imam Husaini (a.s), bal a shar'ance yakamata a kashe Imam Husaini (a.s), da makamantansu – kamar yadda bayanansu zasu zo-, dan uwa mai karatu nasan cewa kai shaida ne akan wannan, a Nigeria ma kaji wani a cikinsu yana cewa an kashe Husaini, SO WHAT? Har zuwa cewa ya kamata a kashe 'yan bidi'a masu juyayi a kan Husaini da sauransu, kuma wannan ittijahin bai gushe ba yana qoqari 'bi kulli ma utiya min quwwa' ya nemawa ra'ayoyin sa gindin zama a addinin musulunci, bal sune musulunci da sunnanci, wanda wannan yakan rudi wasu ko sa shakka a kwakwalan wasu, saboda haka yakamata mu mahimmantar da bincike akan tunane-tunanen wannan ittijahin da kuma dora su akan mizani na karatu, saboda a cikin haka akwai khidimtawa ga ilimi a fikril'islami da kuma khidimtawa ga society din musulmi. Kafin mu shiga bayanin abubuwan da salafiyah suke cewa akan Imam Husaini (a.s) da tsayuwar Sa zamu gabatar da wasu bahasosi guda biyu saboda su zama shinfida. NA FARKO: HUSAINI DAGA GARENI YAKE NIMA DAGA HUSAINI NAKE. NA BIYU: TSAYUWAR IMAM HUSAINI (A.S). HUSAINI DAGA GARENI YAKE NIMA DAGA HUSAINI NAKE. Kafin in shiga a cikin wannan bahasin akwai buqatar in sanar da dan uwa mai karatu manhajina wato hanyar da nake bi a gurin naqalto hadisi a rubuce-rubucena, saboda ya samu sauki gurin yin raddi da naqadin abun da yake ciki. Na farko: Isnadin sa ya zama SAHIHI (li zatihi ko li ghairihi) ko HASAN (li zatihi ko li ghairihi) Na biyu: Ya zama SARIHI wato abun da nake so in tabbatar a bayyane yake a cikinsa.

Na uku: Ya zama MUJMA'AN ALAIHI BAINAL MADRASATAINI wato sunnah da shi'a sun karbe shi kuma sun yarda dashi. Wannan kuma saboda fadar Manzon Allah (SAWA) cewa Al'umma ta bata haduwa akan bata ko kuskure. Wannan ba wata munaqasha a kan sa shi'a ko a sunnah kamar yadda ya tabbata a muhallinsa. Akan asasin wannan baya inganta ga wani ya kafa ma abokin tattaunawar sa hujja da abun da ya kebanta da shi a littafan sa ba tare da la'akari da na abokin sa ba, saboda wannan ba zai zama hujja a kan kowa da kowa ba, bal hujja ce a kan wanda yazo a littafan sa, wannan shine jawabin ishkalin da wasu suke tadawa cewa shi'a na zabi sonka a littafan sunnah, la wallah muna naqalto wanda muka yi ittifaqi mu da ku a kansa ne, domin shine hujja a kan kowa, amma wanda bama naqaltowa hujja ce akan ku saboda a littafanku kawai yazo, kamar yadda wanda yazo a littafanmu hujja ce a kanmu kawai. Dan uwa mai karatu hadisin da nake so inyi Magana akai a wannan bahasin ya tattara wadannan sharuddan guda uku, ga bayanin kamar haka: HADISIN DA ISNADINSA ALHAKIMUT'TIRMIZI حدثنا الحسن بن عرفة حدثنا إسمعيل بن عياش عن عبد الله بن عثمان بن خثيم عن سعيد بن راشد عن يعلى بن مرة قال : قال ) رسول

الله صلى الله عليه وسلم ) : حسين مني وأنا من

حسين أحب الله من أحب حسينا حسين سبط من الأسباط . ثم قال : هذا حديث حسن وإنما نعرفه من حديث عبد الله بن عثمان بن خثيم، وقد رواه غير واحد عن عبد الله بن عثمان بن خثيم . Daga Abdullahi ibn Usman ibn khathaimi daga Sa'idu ibn Rashid daga Ya'ala ibn Murra yace: Manzon Allah (s.a.w.a) yace: Husaini daga gareni yake Ni kuma daga Husaini nake, Allah yana son duk mai son Husaini, Husaini sibtun ne daga cikin Asbaat. Sannan sai tirmizi yace: WANNAN HADISINE HASAN, kuma mun san hadisin ne kawai ta hanyar Abdullahi ibn Usman ibn khathaimi, kuma haqiqa mutane da yawa sun ruwaito sa daga Abdullahi ibn Usman ibn khathaimi. Allamah Albani shima ya yarda da zaman wannan hadisin hasan (a duba: Sahihu Wa dha'ifu Sunanit Tirmizi, bugun Iskandariya: Markazu nuril Islam Li Abhaasil Qur'ani Was Sunnah, juzu'i na 8, shafi na 275, hadisi na 3775). IBN MAJAH

عن عبد الله بن عثمان ابن خثيم عن سعيد بن أبي راشد أن يعلى بن مرة حدثهم أنهم خرجوا مع النبي ) صلى الله عليه وسلم ( إلى طعام

دعوا له فإذا حسين يلعب في السكة، قال

: فتقدم النبي ) صلى الله عليه وسلم ( أمام القوم وبسط يديه فجعل الغلام يفر ها هنا وها هنا ويضاحكه النبي ) صلى الله عليه وسلم (

حتى أخذه فجعل إحدى يديه تحت ذقنه والأخرى في

فأس رأسه فقبله وقال : حسين مني وأنا من حسين أحب الله من أحب حسينا حسين سبط من الأسباط . و حدثنا علي بن محمد حدثنا وكيع

عن سفيان مثله

. Daga Abdullahi ibn Usman ibn khathaimi daga Sa'idu ibn Abi Rashid daga Ya'ala ibn Murra ya basu labari cewa sun fita tare da Manzon Allah (s.a.w.a) zuwa cin wani abinci da Yayi gayyata, sai suka tarar da Husaini Yana wasa a hanya, sai Manzon Allah Ya shiga gaban mutane Ya bude hannayen Sa Yana son ya kama Husaini, sai Husaini Ya rinqa yin nan da can baya so ya kama Shi, Shi kuma Manzon Allah Yana ta sanya Sadariya har Ya kama Shi, sai Ya sanya dayan hannun sa a habarsa, dayan kuma a tsakiyar kan Sa sai Ya sumbance Shi, sai yace: Husaini daga gareni yake Ni kuma daga Husaini nake, Allah Yana son duk mai son Husaini, Husaini sibtun ne daga cikin Asbaat. Allamah Albani yayi masa qarin haske da cewa: wannan hadisin hasan (aduba: Sahihu Wa Dha'ifu Sunani Ibn Majah, bugun Iskandariya: Markazu nuril Islam Li Abhaasil Qur'ani Was Sunnah, juzu'i na 1, shafi na 216, hadisi na 144).

Wannan kenan sannan ibn hibban ya inganta wannan hadisin (a duba: Sahihu ibn Hibban, tahqiqin Shu'aibu Arna'ut, bugun Mu'assasatur'risala, Juzu'i na15, Shafi na 427 – 328, hadisi na 6971). sai mun hadu a bahasi na gaba Wassalamu alaikum.

Littattafan da aka duba:

1). Sahihu ibn Hibban

2). Sahihu Wa Dha'ifu Sunani Ibn Majah.

3). KAMILUZ ZIYARA na Allamah Jafar Muhammad ibn Qulawih.

4). Silsilatul Ahadisis Sahiha.

5). Kanzul'ummal Fi Sunanil Aqwal Wal Af'al, Tahaqiqin Bakari'hayyani.

6). Assawa'iqul Muhriqa Ala Ahlil'Rafdi Waz'Zandaqa, Tahqiqin Abdurrahman ibn Abdullah Atturki da Kamil Muhammad Alkharat.

7). Majma'uzzawa'id Wa Manba'ul fawa'id