Rashin jirkitar Alkur'ani mai tsarki na 2
RASHIN JIRKITAR AL-KUR'ANI
A tafsirin Qurdabi da Durul'manthur dukkan su suna daga cikin fitattun littattafan tafsirin ahlus sunna, an naqalto daga A'isha (matar Annabi [SAWA]) tana cewa:
«انها - اى سورة الأحزاب – كانت مأتى آية فلم يبق منها إلا ثلاث و سبعين!»[1]
Suratul Ahzab ta kasance tana da ayoyi 200 ne, amma yanzu banda ayoyi 73 babu abin da yayi saura.
Bayan wannan akwai wasu ruwayoyi a cikin sahih Bukhari da sahih Muslim wadanda suke nuna alamun tahrif (jirkitar Alqur'ani).[2]
Amma mu ba zamu taba baiwa kanmu dama cewa mu dangantawa 'yan uwa ahlus sunna yarda da jirkitar Alqur'ani, kawai saboda wani marubuci guda daya ko kuma saboda wasu 'yan ruwayoyin da suke raunana, kuma suma bai kamata ba saboda littafin mutun daya ko kuma wasu hadisai raunana wadanda gungun manyan malaman Shi'a sun baranta dasu, su yiwa shi'a hukumci dasu.
Rubutu da ruwayoyin littafin Faslul khidab na Ha'ji Nuri kacokan sun zo ta hanyar masu ruwaya uku ne kacal kuma su duka ukun a cikin su daga wanda yake mai gurbatacciyar aqida sai maqaryaci sai kuma wanda ba a san halin shi ba (Ahmad bin Muhammad As'sayyari mai gurbatacciyar aqida, Ali bin Ahmad Kufi maqaryaci da Abil Jarud ba a san shi ba ko kuma ana da shakka akan shi).[3]
KADA GABA KO QIYAYYA TA BAMBANCIN MAZHABA TA SA KU SARI TUSHEN (JIJIYA) MUSULUNCI DA GATARI
Wadanda suka dage akan tuhumar Shi'a da aqidar jirkitar Alqur'ani basu san cewa a dalilin gaba ta mazhaba, suna sarawa saiwar musulunci gatari bane, saboda haka maqiya na waje suke cewa: Rashin jirkitar ko cikar Alqur'ani a tsakanin musulmai ma ba korarre bane, saboda gungu babba daga cikin su suna da aqidar rashin cikar Alqur'ani. Dan haka muna yiwa 'yan uwa nasiha cewa, kada tsananin bangarenci da qiyayya da tsananin ta'asubanci, susa ku mayar da zuciyar musulunci wato Alqur'ani ya zama abin kaiwa hari.
Kuzo ku jiqan musulunci da Alqur'ani sannan ku daina kawo maganar jirkitar Alqur'ani dan kada ku baiwa maqiya qofa ko damar da zasu ci mutuncin addinin mu.
Wannan tuhuma da batanci har sun kai matuqa cewa a wata tafiya da muka yi zuwa Umara, da muka hadu da shugaban al'amuran addini na Saudiya bayan ya tarbe mu sai kuma yace: Naji ance kuna da Alqur'ani ba irin wanda muke dashi ba!!
Sai nace gwajin haka yana da matuqar sauqi, yanzu kai da kanka ko kuma ka hada mu da wani wakilin ka mu koma zuwa Tehran (mun dau nauyin zuwa da dawowa da duk wata dawainiya), akwai alqur'ani a dukkan masallatai da gidaje, akwai dubunnan masallatai da dubunnan xaruruwan gidaje a Tehran, zabar gida ko masallaci yana hannun wakilin naka, sai mu buga qofa mu nemi a kawo mana Alqur'ani, sai ka gani akwai kalma daya a ciki da ta bambanta da ta sauran Alqur'anin da suke a sauran qasashen musulmi; babban malami irin ka bai kamata ace ya yarda da irin wannan jita-jitar ba!
Masu qira'ar mu sun sha daukar matsayi na farko a gasar karatun Alqur'ani da ake shiryawa na duniya, sannan kuma mahaddatan mu, musamman ma mahaddata yara, sun matuqar girgiza duniyar musulmi da samun yabo daga da yawa daga qasashen musulmi.
A kowacce shekara muna samun qaruwar dubunnan mahaddata da masu qira'a ne, sannan kuma ajujuwan Hadda, Qira'a, Tafsirin Alqur'ani da kwaleji-kwaleji na Ulumul'qur'an sun mamaye faffadar qasar mu, kuma tabbatar da duk wadannan shirye-shirye abu ne mai sauqi ga kowa.
A duk wadannan gurare babu wani Alqur'ani da ya wuce shi dai wannan Alqur'ani da yake a hannun dukkan musulmin duniya, kuma babu wani da ya san wani Alqur'ani bayan wannan kuma babu wani majlisi ko taro da ake batun jirkitar Alqur'ani.
DALILAI NA HANKALI DA NASSI AKAN RASHIN JIRKATAR ALQUR'ANI MAI TSARKI
Mu munyi imani da akwai dalilai na hankali da kuma Nassi masu yawa da suke nuni akan rashin jirkitar Alqur'ani, saboda a bangare guda Alqur'ani mai tsarki yana cewa:
إِنَّا نحَنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَ إِنَّا لَهُ لحَافِظُونَ
Mu muka saukar da ambato (Alqur'ani) kuma kiyaye shi na hannun mu.[4]
Sannan a wani gurin yana cewa:
إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُواْ بِالذِّكْرِ لَمَّا جَاءَهُمْ وَ إِنَّهُ لَكِتَابٌ عَزِيزٌ41
لَّا يَأْتِيهِ الْبَاطِلُ مِن بَينِْ يَدَيْهِ وَ لَا مِنْ خَلْفِهِ تَنزِيلٌ مِّنْ حَكِيمٍ حَمِيد 42.
41. Waɗannan da suka kãfirta game da Alkur'ãni a lõkacin da ya je musu, kuma lalle shi haƙĩƙa littãfi ne mabuwãyi.
42. Ɓarna bã zã ta je masa ba daga gaba gare shi. kuma bã zã ta zo ba daga bãya gare shi. Saukarwa ce daga Mai hikima, Gõdadde.[5]
Shin littafin da Allah da kanshi Ya dau nauyin kiyaye shi, wani ya isa ya iya jirkita shi?!
Ta kuma daya hannun shi Alqur'ani ba littafi bane yasasse wato wanda aka manta dashi ba a yawan amfani dashi wadda har wani zai iya qara ko rage wani abu daga cikin shi.
Marubuta Wahayi wadanda yawan su daga 14 sun kai kusan mutun 400 sun rubuta, da zarar aya ta sauka suke rubuta ta kuma su adana ta.
Akwai daruruwan mahaddata Alqur'ani a lokacin Annabi (SAWA) wadanda ayoyi na sauka suke haddace su.
Qira'ar qur'ani a wancan zamani tana daga cikin mafi muhimmancin ibada, dan haka dare da rana tilawa akeyi.
Qari akan wadannan qur'ani shine dokoki na asali na addinin musulunci da rayuwar musulmai, dan haka yana cikin dukkan rayuwar su.
Dan haka hankali da tunani suna hukumta cewa, ba zai taba yiwuwa ba littafin da yake da wadannan sifofi ya jirkita wato ba zai yiwu ya sami qari ko ragi ba.
Ruwayoyin musulunci da suka zo mana daga Imamai tsarkaka (AS) suna qarfafa da tabbatar da cikar wannan littafi mai tsarki.
Amirul muminina Ali (AS) a Nahjul balagha yana cewa:
«أنزل عليكم الكتاب تبيانا لكل شيء و عمر فيكم نبيه أزمانا حتى أكمل له و لكم فيما أنزل من كتاب، دينه الذي رصى لنفسه.
Allah Ya saukar da Alqur'ani wadda yake yin bayanin komai, Allah Ya raya Annabi (SAWA) har zuwa lokacin da Yaga ya kammala muku addinin Shi ta hanyar qur'ani.[6]
A da yawa daga hudubobin Nahjul balagha akwai maganganu da suka akan qur'ani, kuma babu gurin da komai qanqantar shi akayi ishara da jirkitar qur'ani, sai ma tabbatar da cikar shi suke yi.
A wani hadisi wadda Imam na tara, Muhammad bin Ali At'Taqiy (AS) yake magana da daya daga cikin sahabban shi dangane da kaucewar mutane daga hanyar gaskiya yana cewa:
و كان من نبذهم الكتاب أن أقاموا حروفه و حرفوا حدوده.
Wani gungu daga cikin mutane sun bar qur'ani, lallai Alqur'ani yana nan kamar yadda yake, kawai sun canja fahimta shi ne.[7]
Irin wannan hadisin da makamantan shi suna nuna cewa lafuzan qur'ani suna nan kamar yadda suke, a ma'ana ne wasu suke fassara ayoyin qur'ani bisa san ran su.
Dan haka daga nan zamu fahimci cewa idan a wasu ruwayoyi aka yi magana akan jirkitar qur'ani, to ana nufin jirkita a ma'ana ne da tafsiri bisa ra'ayi da son zuciya ba wai jirkita a rubutu da lafuzan qur'ani ba.
A wani bangaren kuma a da yawa daga ruwayoyi ingattattu da suke zuwan mana daga Imamai tsarkaka (AS) muna karantawa kamar haka: domin gane gaskiya ko akasin haka akan ruwayoyi, musamman a lokacin da aka sami karo da juna a tsakanin ruwayoyi, to ku dauke su ku dora su akan qur'ani (wato ku auna su dashi), wacce ta dace da qur'ani itace daidai, wadda kuma ta sabawa qur'ani ba daidai bace sai ku ajiye ta.
اعرضو هما على كتاب الله فما وافق كتاب الله فخذوه و ما خالف كتاب الله فردوه.[8]
Wannan dalili ne a fili da yake nuna rashin jirkitar qur'ani, inda ba haka ba to da ba a sanya shi a matsayin sikeli (ma'auni) na gane gaskiya daga bata ba.
Qari akan duk wadannan shine, fitaccen hadisin Saqalain (nauyaya biyu) wadda yazo da yawa a cikin littattafan Shi'a da ahlus sunna, yazo kamar haka;
قال رسول الله (صل الله عليه و آله): إنى تارك فيكم الثقلين كتاب الله و عترتى أهل البيتي ما إن تمسكتم بهما لن تضلوا.
Manzan Allah (SAWA) yana cewa; Na bar muku nauyaya (wato abubuwa guda biyu masu qima) littafin Allah da ahli baiti na idan kuka yi riqo dasu to ba zaku taba bacewa ba.[9]
Wannan hadisi mai ma'ana yana nunawa da kyau cewa Alqur'ani mai tsarki da kuma Ahlil baitin Annabi (SAWA) a tare dashi mafaka ne masu matuqar nagarta wajen shiryar da mutane har zuwa ranar Alqiyama.
Idan da qur'ani ya kasance za a iya jirkita shi, da ba zai taba kasancewa madogarar da zai kare mutane daga bata ba.[10]
Magana ta qarshe
Magana ta qarshe itace daya daga cikin manyan zunubai a gurin Allah shine tuhumar mutane akan al'amarin da basu taba fada ko aikatawa ba.
Mu a ko'ina mun fada kuma muna qara faxe cewa babu wani daga cikin manazarta da manyan malaman Shi'a - da shaidar littattafansu – da suka yarda da jirkitar qur'ani, amma wasu rukunin mutane masu ta'asubanci da taurin kai, sai maimaita wannan tuhumar suke yi, ba a san wacce amsa suka tanada ba ranar gobe qiyama sakamakon tuhuma da kuma raunata qur'ani da suke yi.
Idan kuna fakewa da wasu ruwayoyi raunana da suka zo a wasu littattafan mu ne, to akwai irin wadannan ruwayoyi raunana a cikin littattafan hadisi da tafsirin ku.
Babu wata mazhaba da zata kafu ko dogara da ruwayoyi raunana, mu ba zamu taba sakamakon littafin Alfurqan fi tahrifil qur'an na ibnil khadib misri da waxancan ruwayoyi raunana da kuke dasu akan jirkitar qur'ani, ba zamu tuhume ku da yarda da jirkitar qur'ani ba, kuma ba zamu taba cin fuskar qur'ani haka ba.
Ku bar fadar wannan magana ta jirkitar qur'ani, kada ku zalumci musulunci da musulmai da kuma qur'ani, kuma kada a dalilin ta'asubancin mazhaba ku ragewa qur'ani wadda yake jarin asalin musulmin duniya, qima, ta hanyar maimaita kalmar tahrif (jirkita), kada ku bayar da dama ga maqiya, ku sani cewa idan kuna ganin kuna so ku dauki fansa akan shi'a da mabiya ahlil baiti (AS) ne, to ku sani cewa kuna sharewa maqiya fagen girgiza tushen musulunci ne ba tare da kun sani ba, saboda suna cewa wasu gungu da yawa daga musulmai sun yarda da jirkitar qur'ani, wannan babban zalumci ne ga qur'ani mai tsarki.
A qarshe muna qara cewa a fili babu wani daga manazartan shi'a da ahlus sunna da ya yarda da jirkitar qur'ani, kuma qur'anin da aka saukarwa da Annabi (SAWA), da wanda yake a hannun al'ummar musulmai a yanzu haqiqa daya ne babu wani bambanci, kuma kamar yadda yazo a cikin qur'anin a fili cewa Allah da kanshi ya dau nauyin kare shi daga dukkan canji kojirkita. Amma sai kaga wasu masu ta'asubanci da rashin ganewa daga dukkan bangarori biyu suna mantara da tuhumar juna da aqidar jirkitar qur'ani, abin takaici basu san suna cirewa juna qaho bane.
Allah Ya ganar dasu duka.
Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.
[1] تفسير قرطبى، جلد 14، صفحة 113، و تفسير الدر المنثور، جلد 5، صفحة 180.
[2] صحيح بخارى، جلد 8، صفحة 208 الى 211 و صحيح مسلم، جلد 4، صفحة 167 و جلد 5، صفحة 116.
[3] Domin samun cikakken bayani akan wadannan mutun uku, za a iya duba littafin Rijal na Najashi da sauran littattafan Rijal.
[4] Suratul Hijr, aya ta 9.
[5] Suratu fussilat, aya ta 41 da 42.
[6] Nahjul balagha, huduba ta 86.
[7] Al-ka'fi, mujalladi na 8, shafi na 53.
[8] Wasa'il' shi'a, mujaladi na 18, shafi na 80
[9] Biharul anwar, mujalladi na 36, shafi na 331.
[10] Domin qarin bayani akan wannan za a iya duba littafin mu انوار الاصول mujalladi na biyu