Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Aqida

Taqiyya a Littafi da Sunna

2016/04/18

Taqiyya a Littafi da Sunna

TAQIYYA A LITTAFI DA SUNNA

Monday, April 18, 2016

9:56 PM

Wani batu wanda shima masu neman fakewa da ta\'asubanci, masu neman aibun mabiya mazhabar Ahlil baiti (AS), suke kwayayato akai shine batun Taqiyya; suna cewa me yasa kuke yin Taqiyya? Shin Taqiyya ba nau\'i ne na munafunci ba?!

Suna kambama wannan batun, kai kace taqiyya wani aikin haramun ne ko babban zunubi ko ma sama da hakan.

Sun manta cewa qur\'ani mai tsarki a wasu ayoyi, tare da wasu sharuda kebabbu ya halatta ta, da kuma ruwayoyin da suka zo a cikin littattafansu suma suna tabbatar da ita, qarin a kan haka, taqiyya da dukkan sharudan ta umarni ne bayyananne na hankali, kuma da yawa daga cikin su sun taba aikata ta a rayuwar su ta yau da kullum.

Domin qarin bayani dangane da wannan batu, bari mu dubi wasu bayanai kamar haka:

Mecece Taqiyya?

Idan aka ce Taqiyya ana nufin cewa mutun ya boye aqidar shi ta addini a gaban maqiya masu ta\'asubanci da tsanani wadanda zasu iya cutar dashi.

Misali ace ga wani musulmi ya sami kanshi a tsakanin wasu mushrikai mugaye, wadda idan ya bayyana imanin shi a fili hakan zai sa mutuncin shi, dukiyar shi da ma rayuwar shi su kasance cikin hadari a gurinsu, to sai ya boye aqidar shi ta badini domin ya tsira daga cutarwar su.

Ko kuma wani musulmi dan shi\'a ya sami kanshi a hannun wahabiyawa masu tsattsauran ra\'ayi wadda suka dauki zubar da jinin dan shi\'a ya halatta a gurin su, a cikin jeji ko saharar da babu kowa, a wannan halin domin kare dukiya, mutunci da rayuwar shi sai ya boye aqidar shi.

Duk mai hankali zai yarda cewa wannan aiki da suka yi ya dace da hankali. Kuma hankali yana hukumta haka cewa dan me zaka fansar da ranka ga masu wuce iyaka \'yan dabar addini.

Bambancin Taqiyya da Munafunci

Munafunci kishiyar (akasi) Taqiyya ne, Munafuki shine wanda a boye (badini) baiyi imani da rukunnan musulunci ba ko kuma yana yin shakka akan su, amma a cikin musulmai sai ya riqa nuna shi musulmi ne na qwarai.

Ita kuma Taqiyya da muke fada itace mutun yana da imani na haqiqa a badinin (boye) shi, amma sakamakon aqidar wasu masu wuce iyaka kamar wahabiya wadanda banda kansu basu yarda da musuluncin sauran musulmai ba, kuma har suna yi musu barazana; to duk lokacin da mutun mai imani ya boye aqidar shi a gare su domin kare dukiya, mutunci da ranshi, shi ake cewa Taqiyya, wato kishiyar munafunci ce.

Taqiyya a ma\'aunin hankali

Taqiyya a haqiqance garkuwa ce abun kariya, kuma saboda haka ne ma a ruwayoyin mu tazo da sunan «تٌرس المؤمن» wato Garkuwar masu imani.

 

Babu hankalin da zai bayar da dama mutun ya bayyana aqidar shi ta boye ga wani mugun mutumin da zai jawo salwantar dukiya, mutunci ko ranshi, saboda bata qarfi ko kayan aiki a gurin da babu amfani, abu ne da ya sabawa hankali.

 

Taqiyya tayi kama da salo ne ko dabaru wadda sojoji suke amfani dasu a fagen daga (filin yaqi), wato boye kawukansu da suke yi a cikin bishiyoyi da ramukan da suke haqawa da kuma bayan buhunan yashi daga abokan gaba, haka za kuga sun sanya tufafi masu sajewa da kalar rassan bishiya, duk dan kada su bayar da jinin su haka kawai cikin araha.

 

Dukkan mahalkantan duniya suna yin amfani da salon Taqiyya domin tsare rayukan su daga maqiyansu, kuma ba za a taba hana wani yin amfani da wannan hanyar ba. A duk duniya ba zaku taba samun mutumin da zai qi karbar taqiyya da dukkan sharuxan ta ba.

Taqiyya a littafin Allah mai tsarki

 

A cikin Alqur\'ani mai tsarki ayoyi da dama sun nuna halaccin yin taqiyya ga kafirai da maqiya. Bari mu kawo wasu daga cikin su:

 

A labarin Muminin gidan fir\'auna muna karantawa kamar haka:

 

وَ قَالَ رَجُلٌ مُّؤْمِنٌ مِّنْ ءَالِ فِرْعَوْنَ يَكْتُمُ إِيمَانَهُ أَ تَقْتُلُونَ رَجُلاً أَن يَقُولَ رَبىّ‏َِ اللَّهُ وَ قَدْ جَاءَكُم بِالْبَيِّنَتِ مِن رَّبِّكُمْ...

 

 

Kuma wani namiji mũmini daga dangin Fir\'auna, yanã bõye ĩmãninsa, ya ce: "Ashe, za ku kashe mutum dõmin ya ce Ubangijina Allah ne, alhãli kuwa haƙĩka ya zo muku da hujjõji bayyanannu daga Ubangijinku?... [1]

 

Sai ya cigaba da cewa: Ku qyale shi da halin shi, idan abin da yake fada qarya ne, to ai shi kadai qarya zata ci, idan kuma gaskiya yake fada, to kunga akwai yiwuwar wasu daga cikin azabobin Ubangiji da yake gargadin ku akan su, su same ku.

 

Da wannan salon Muminin gidan fir\'auna ta hanyar boye imanin shi, ya riqa yiwa wadancan hatsabiban mutanen da suka yanke shawarar zubar da jinin Annabin Allah Musa (AS), nasihohin da suka kamata.

 

A wani gurin kuma a cikin qur\'ani mai tsarki muna karantawa:

 

لَّا يَتَّخِذِ الْمُؤْمِنُونَ الْكَافِرِينَ أَوْلِيَاءَ مِن دُونِ الْمُؤْمِنِينَ وَ مَن يَفْعَلْ ذَالِكَ فَلَيْسَ مِنَ اللَّهِ فىِ شىَ‏ْءٍ إِلَّا أَن تَتَّقُواْ مِنْهُمْ تُقَئة...

 

 

Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da \'yar kãriya...[2]

 

Wannan ayar tana hani da yin abota da maqiya na haqiqa, sai dai a yayin da barin abotar, zai jawo cutuwa ga musulmai, wato anan sai ayi amfani da abotar a matsayin taqiyya ko wata garkuwa ta kare kai.

 

Sannan labarin Ammar Yassir da Mahaifiyar shi da Baban shi, dukkan masu tafsiri sun naqalto cewa, wadannan mutun ukun da suka fada hannun mushrikan Makka marasa tausayi, suka tilasta musu da suyi wa Annabi (SAWA) bara\'a, mahaifiya da baban ammar suka qi yi, aka shahadantar dasu, amma shi Ammar a bisa Taqiyya sai ya fadi abin da mushrikan suke so, sannan daga baya cikin kuka ya tafi gaban Annabi (SAWA). A wannan lokacin sai wannan ayar mai tsarki ta sauka:

مَن كَفَرَ بِاللَّهِ مِن بَعْدِ إِيمَانِهِ إِلَّا مَنْ أُكْرِهَ وَ قَلْبُهُ مُطْمَئنِ‏ُّ بِالْايمَان‏...

 

Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni...[3]

 

Annabi (SAWA) ya kira mahaifan Ammar da shahidai, sannan ya sharewa Ammar hawaye daga idanun shi yace dashi babu aibu a tare da kai, idan suka kuma tirsasa ka akan wadannan kalaman, to ka qara fada!

 

Dukkan masu tafsiri sun hadu akan cewa dangane da saukar wannan aya ta sama akan Ammar da mahaifan shi da kuma maganganun da Annabi (SAWA) yayi, yana nuna cewa al\'amarin Taqiyya karbabbe ne ga kowa. A gaskiya akwai matuqar daure kai sosai ace duk da wadannan sanadi mai qarfi da kalaman malaman tafsirin Ahlus sunna, amma sai su riqa sukar shi\'a saboda sun yarda da Taqiyya?!

 

Dan haka, Ammar da Muminin gidan Fir\'auna ba wanda yayi munafunci a cikin su, hasali ma sunyi amfani da Taqiyya ne kamar yadda Allah Ya umarta.

Taqiyya a ruwayoyin musulunci

 

A cikin ruwayoyin musulunci ma Taqiyya ta kama gurare masu fadin gaske kamar haka:

 

Musnad Abi shaiba yana daga cikin sanad fitattu na Ahlus sunna. A cikin labarin Musailama kazzab, ya naqalto yana cewa, wani lokaci Musailama kazzab ya kama mutun biyu daga cikin sahabban Manzan Allah (SAWA), a yankin da yake da dan qarfi. Sai ya tambaye su yace Shin zaku shaida cewa ni ma\'aikin Allah ne?! Sai daya ya shaida sai aka sake shi, shi kuma dayan yaqi sai aka sare kan shi.

 

Da labarin ya sami Annabi (SAWA) sai yace: wanda aka kashe ya yi taku akan hanyar gaskiya, hanya madaidaiciya shi kuma na biyu ya karbi rangwamen Ubangiji kuma babu sabo ko aibu gare shi.[4]

 

A hadisan Imaman ahlul baiti (AS) musamman ma Imaman da suka rayu lokacin mulkin banu umayya da banu abbas lokacin da duk inda aka sami masoyan Imam Ali (AS) ana kashe su, za a ga umarni da yin Taqiyya da yawa a waccan lokutan, saboda daukar nauyin kare rayukan su daga sharrin wadancan sarakuna marasa imani da tausayi, sai suka riqa yin amfani da garkuwar Taqiyya.

Shin Taqiyya ana yin ta ne ga Kafurai kadai?

 

Wasu daga cikin maqiya a yayin da suka ga sun sami kansu a saman ayoyi bayyanannu da ruwayoyi dangane da batun Taqiyya, suka ga cewa babu wani zabi illa amincewa da shar\'ancin wato halascin Taqiyya a musulunci, sai kuma kaji suna cewa ai Taqiyya ga kafirai kadai ta halatta wato baya halatta a yi ta ga musulmai.

 

Ta yin la\'akari da dalilan da muka ambata a baya zamu ga rashin bambancin yin ta ga duka biyun a fili, saboda:

 

Idan ma\'anar Taqiyya shine kare dukiya, mutunci da kuma Rai daga barazanar mugaye ko masu keta hurumin dan adam - kuma akwai su din – to menene bambanci tsakanin musulman da basu san abin da suke yiba wato wawayen musulmai masu ta\'asubanci, da kuma kafirai? Idan hankali da tunani suna hukumta kare kai daga wannan al\'amari da tsoratarwar su mara amfani, to ina bambanci yake a tsakanin su biyun?

 

Mu muna magana ne akan wadanda a sakamakon baqin jahilci da yin amfani da labaran qarya da batanci suke cewa: zubar da jinin dan shi\'a aiki ne da yake kusantar da mutun ga Allah, shin idan dan shi\'a na haqiqa mabiyin Amir al-muminin Ali (AS) da ahlul baitin Annabi (SAWA) ya sami kanshi a tsakanin wadancan sai suka tambaye shi meye mazhabar ka? Cikin sauqi sai yace dasu ni dan shi\'a ne? Kawai su sare mashi kai da baqin jahilcin su?!

 

Akwai wani mai hankali da tunani da zai yi hukumci da haka?!

 

Ta wata fuskar idan abin da mushrikan larabawa suka yiwa Ammar yasir, ko kuma abin da mabiyan musailama kazzab suka yiwa sahabban nan na Annabi (SAWA) guda biyu, da abin da sarakunan umayyawa da kalifofin banu abbas da makamantansu daga cikin wawayen masulmai, suke yiwa \'yan shi\'ar Ali (AS), yanzu da duk wannan ya kamata muyi hukumci da haramcin Taqiyya wadda hakan zai jawo musabbabin salwantar daruruwa ko dubunnan rayukan mabiya Ahlul baitin Annabi (SAWA) na haqiqa, kawai saboda a zahiri wadancan sarakunan musulmai ne?!

 

Idan da ace Imaman ahlul baiti (AS) basu qarfafa batun Taqiyya da yawa ba, kamar yadda suka ce تسعة أعشار الدين التقية wato tara cikin goma na addini Taqiyya ne.[5], da babu mamaki adadin \'yan shi\'ar su da za a kashe a lokacin banu umayya da banu abbas, su kai dubunnan daruruwa ko miliyoyi, wato ninkin ba ninkin kisa na rashin imani da dabbanci da aka yi musu.

 

Shin duk da wannan sai ayi tardidi ko shakka akan shar\'anci ko halascin yin Taqiyya?!

 

Ba zamu manta ba cewa ahlus sunna ma a wasu shekaru sakamakon sabanin mazhaba, a dunqule akan batun Ha\'dis ko Qadim[6] din qur\'ani, sunyi fada mai tsanani akan haka wadda har ya haifar da zubar da jini mai yawa! (wadda wannan fada a yau manazarta sun fassara shi da fada mara ma\'ana wanda bashi da amfani ko daya).

 

Shin bangare ko qungiyar da suka san cewa akan gaskiya suke, idan suka sami kansu a hannun maqiyan da zasu cutar dasu, idan suka tambaye shi dangane da aqidar shi, sai kawai yace musu kaza ce aqida ta? Koda kuwa za su sheqar da jinin shi? Wadda a gurinsu qaramin aiki ne?!

 

Fakhri Razi a tafsirin wannan ayar mai tsarki       إلا أن تتقوا منهم تقاة [7] yana cewa: zahirin wannan aya yana nuni akan cewa Taqiyya ga kafirai shine tafi zama daidai, «إلا أن مذهب الشافعى - رض- أن الحالة بين المسلمين إذا شاكلت الحالت بين المسامين و المشركين حلت التقية محاماة على النفس» wato a mazhabar shafi\'i yadda batun yake shine idan yanayin al\'amarin musulmai ya kasance kamar na tsakanin su da kafirai, to yin Taqiyya domin tsare rai ya halatta.

 

Sannan kuma dalilin halascin yin Taqiyya domin tsare dukiya, shine hadisin Annabi (SAWA) da yake cewa: «حرمة مال المسلم كحرمة دمه» wato martaba dukiyar musulmi kamar martaba jinin shi ne. Da kuma hadisin: «من قتل دون ماله فهو شهيد» wato wanda aka kashe shi a wajen kare dukiyar shi, ya mutu shahidi.[8]

A tafsirin Nishaburi wadda yazo a ha\'shiyar (qarin bayanin marubuci) tafsirin Dabari shima yana cewa: قال الامام الشافعى «تجوز التقية بين المسلمين كما تجوز بين الكافرين محاماة عن النفس» wato yin Taqiyya domin kare rai ya halatta a tsakanin musulmai kamar yadda ta halatta a tsakanin musulmai da kafirai.[9]

Wani abin jan hankali shine a lokacin kalifancin banu Abbas, wasu daga cikin masana hadisi na ahlus sunna sakamakon takura musu da sarakunan banu abbas suka yi akan aqidar su ta yarda da kasancewar qur\'ani qadimi, sai suka yi Taqiyya suna cewa qur\'ani ha\'dis (fararre) ne, domin tsira daga cutuwa.

 

Ibn Sa\'ad sanannen malamin tarihin ahlus sunna ne, a littafin Dabaqat da kuma Dabari shima sanannen malamin tarihin ahlus sunna ne, a littafin shi na tarihi, sunyi ishara da wasu wasiqu guda biyu daga Ma\'amun dangane da wannan ya aika zuwa ga shugaban dogarawa (\'yan doka) na Bagdad mai suna Ishaq bin Ibrahim.

Abin da ya qunshi wasiqa ta farko Ibn Sa\'ad yana rubutawa, Ma\'amun ya rubuta zuwa ga shugaban dogarawa, kamar haka: "ka turo min mutun bakwai daga cikin fitattun malaman hadisi sune: muhammad bin sa\'ad ka\'tib waqidi, abu muslim, yahaya bin mu\'in, zahir bin harb, Isma\'il bin Dawud, Isma\'il bin abi mas\'ud da kuma Ahmad bin Ad\'Durqi". Yayin da aka kawo su gaban ma\'amun sai ya tambaye su a matsayin gwaji cewa, meye aqidar ku dangane da alqur\'ani? Sai dukkan su suka amsa mashi da cewa qur\'ani halitta ne wato fararre ne (Ha\'dis), alhali ra\'ayin da ya shahara a tsakanin malaman hadisi akasin (kishiyar) haka ne wato akan aqidar qur\'ani qadimi ne suke.[10]

Kunga anan sun ji tsoron horo mai tsanani da zasu iya fuskanta daga Ma\'amun, sai suka yi taqiyya suka yarda cewa qur\'ani halitta ne domin su kubuta.

A kuma wasiqa ta biyu ta ma\'amun wadda itama zuwa ga shugaban dogarawan Bagdada ne, Dabari ya naqalto kamar haka: lokacin da wasiqar ma\'amun ta same shi, sai ya tara wasu daga cikin malaman hadisi wadda yawan su ya kai 26, sai ya karanta musu abin da wasiqar ma\'amun ke dauke dashi, sannan ya riqa kiran su daya bayan daya, yana tambayar su da su bayyana mashi ra\'ayi ko aqidar su dangane da qur\'ani, dukkan su banda mutun hudu sai suka amsa mashi da cewa qur\'ani halitta ne wato ba qadimi bane (wato da Taqiyya suka ceci da kawukansu).

Mutun hudun da ba su canja ba sune, Ahmad bin hambal, Sajada, al-qawariri da kuma muhammad bin Nuhu. Sai shugaban dogarawan ya bayar da umarnin a sanya musu sarqa (ankwa) akai su kurkuku, sai kashegari aka kuma kawo su gabanshi, ya kuma maimaita batun da ya gabata jiya akan qur\'ani, sai sajada ya canja wato yace qur\'ani halitta ne, sai aka sake shi, sauran kuma suka dage akan bakar su, sai aka mayar dasu kurkuku.

Kashegari sai aka kuma kawo mutun ukun nan, sai aka samu al-qawariri shima ya sauka daga bakan (ra\'ayin) shi, sai shima aka sake shi, amma sai Ahmad bin hambal da kuma Muhammad bin Nuhu suka dage a matsayar su, sai shugaban dogarawa ya kore su zuwa garin Dardus.[11]

Yayin da wasu gungun mutane suka yiwa wadanda suka yi Taqiyya bore, sun (wadanda suka yi Taqiyyar) kafa musu hujja ne da abin da Ammar Yassir yayi ga kafirai ne.[12]

Duk wadannan suna nuna mana a fili cewa, a yayin da mutun ya sami kanshi a qarqashin takurawa mai tsanani ta maqiya, hanya daya da zai ceci kanshi itace Taqiyya, wato zai iya yin amfani da hanyar Taqiyya ga kafirai ne ko kuma ga musulmai (a lura da wannan sosai).

Taqiyyar da ta haramta

A wasu guraren yin Taqiyya haramun ne, wato a lokacin da wani ko wasu suka qudiri aniyar yin Taqiyya kuma suka boye aqidar mazhabar su, amma sai yin hakan ya kasance zai sanya tushen musulunci cikin hadari ko kuma ya haifar da wani mummunan rauni ga duniyar musulmai, to a wannan gurin dole ne mutun ya bayyana aqidar shi ta gaskiya, duk irin hadari ko cutuwar da hakan ka iya jawo mashi ko masu.

Sannan kuma wadanda suke ganin cewa yin hakan ya zamo halaka kai ne ko jefa kai cikin halaka wato «إلقاء النفس إلى التهلكة» kamar yadda qur\'ani mai tsarki yayi hani da hakan inda yake cewa: «ولا تلقوا بأيديكم إلى التهلكة» [13], lallai masu danganta wannan ayar da wannan bangaren sunyi kuskure matuqa, saboda wannan fahimta tasu tana nuna cewa kenan mutumin da ya kai kanshi filin Daaga (jihadi) yin hakan kisan kai ne wato haramun ne, alhali babu wani mai hankali da zai ce hakan, kuma ta nan zamu fahimta a fili cewa tsayuwar Imam Husaini bin Ali bin Abi Xalib (AS) ga yazidu, wani nauyi ne na addini da Imam ya sauke, sannan kuma Imam bai kebe - koda da sunan Taqiyya ba- da yazidawa da bani umayya \'yan fashin (masu kwacen) kalifancin musulunci, saboda ya san cewa hakan zai haifarwa da duniyar musulunci wani rauni ko illa babba, dan haka tsayuwar shi da shahadar shi sai suka zama qwayar irin farkawar musulmai da kuma ceto musulunci daga hatsarin cutarwar jahiliyya.

Taqiyyar tsantseni

 

Wannan kuma nau\'in Taqiyya ce wadda take, ma\'abota wata mazhaba za su kiyaye da kuma barin wasu ayyuka wadanda ba zasu haifar wa da tushen addini ko mazhabar su matsala ba, domin samar da hadin kai a tsakanin musulmai, wato sai ya kasance suna yin aiki tare da sauran musulman da suka bambanta a wasu aqidun, tare domin kiyaye hadin kan musulmai.

 

Misali mabiya mazhabar Ahlul baiti (AS) a aqidar su babu damar suyi sujada akan dadduma (carpet) dole sai dai akan dutse ko qasa da kuma abin da ta fitar, ta yin riqo da sanannen hadisin Annabi (SAWA) da yake cewa: «جعلت لى الأرض مسجدا و طهورا»  wato an sanya min qasa ta zama gurin sujada da kuma tsarki (Taimama) a gare ni[14]

 

To idan zasu yi salla a masallacin sauran musulmai ko masjid haram ko kuma a masallacin Annabi (SAWA) dake a Madina, saboda su kiyaye da hadin kan musulmai, ba yadda suka iya sai suyi sujada akan Dadduma din, kamar yadda sauran musulman suke yi.

 

To yin haka ya halatta kuma a aqidar mu sallar mutun tayi. To wannan ce ake kira Taqiyyar tsantseni saboda a wannan gurin babu batun tsoron salwantar dukiya ko rai, sai dai kawai tsantseni da kuma kiyayewa da bambance-bambancen sauran musulmai.

 

Zamu kawo qarshen bahasin Taqiyya da maganar daya daga cikin manya magabata:

 

Wani daga manyan magabata dan Shi\'a ya hadu da wani daga cikin shehunnan jami\'ar Al-Azhar ta Misra, sai shehun da sigar tuhuma yace da malamin shi\'ar: Naji ance kuna yin Taqiyya?!

 

Sai malamin Shi\'ar ya bashi amsa kamar haka: «لعن الله من حملنا على التقية» wato Rahmar Allah ta nisanta da wanda ya jawo muke yin Taqiyya!

 wassalmu alaikum wa rahmatullah wa barakatuhu.

Mun kawo muku wannan bahasin ne daga bahasosin Ayatulla Nasir Makarim Shirazi (H)

 

 

 

 

[1] Surar ga\'fir aya ta 28

[2] Surar A\'li Imran aya ta 28

[3] Surar Nahl aya ta 106

[4] Musnad abi shaiba, mujalladi na 12, shafi na 358.

[5] Bihar al-anwar, mujaladi na 109, shafi na 254

[6] Ha\'dis: yana nufin fararre wato abin da yake da farko. Qadim: yana nufin abin da bashi da farko

[7] Surar A\'li Imran aya ta 28.

[8] Tafsiri kabir na Fakhri Razi, mujalladi na 8, shafi na 13

[9] Tafsirin nishaburi (a ha\'shiyar tafsirin Tabari), mujalladi na 3, shafi na 118.

[10] Tabaqat ibn Sa\'ad, mujalladi na 7, shafi na 167, bugun Beirut.

[11] Wani gari ne a Sham a kusa da ruwa (mu\'ujam ul-buldan, mujalladi na 4, shafi na 30).

[12] Tarikh Tabari, mujalladi na 7, shafi na 197.

[13] Surar baqara, aya ta 195.

[14] Sahih bukahri, mujalladi na 1, shafi na 91 da kuma Sunan Baihaqi, mujalladi na 2, shafi na 433 (wannan hadisin yazo a cikin littattafai da dama