Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Sanin Kai

Sanin Kai domin gina Kai

2017/03/18

Sanin Kai domin gina Kai

SANIN KAI

17 March 2017 15:10

SANIN KAI DOMIN GINA KAI NA (1)

 

 

Da sunan Allah mai Rahma mai jin Qai.

Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzanSa Muhammad da Iyalan gidansa tsarkaka.

Za mu fara gabatar da wannan bahasi akan mutum, wato sanin haqiqanin mutum, amma da yake bahasin da alamun zai tsawaita kuma sakamakon rashin wadatar lokaci, da kuma kada yawan Shi a lokaci guda ya gunduri mai karatu; to zamu karkasa shi zai riqa fitowa daki-daki. Kamar haka, wannan ne kashi na farko: Mutum ta fuskoki daban-daban, ya kasance abin la\'akari ko bahasi, wato maudhu\'in ilmomi kala-kala da kowannensu yake bahasin mutum ta fuska daya, kamar: Ilmin sanin dabi\'ar Dan Adam (psychology), ilmin zamantakewar Dan Adam (sociology), Tarihi, Akhlaq, Likitanci, Ilmin rayuwar Dan Adam (biology) ds...wadanda kowanne daga cikinsu ya dauki wani 6angare ne na samuwar mutum yana yin bahasi a kai.

To mu a wannan bahasin za mu yi magana a kan mutum ne ta fuskancin cewa Shi mutum halitta ce ko samuwa wacce take kar6ar Kamala; kuma za mu yi magana ne dangane da kamala ta qololuwa da kuma hanyar isa gare ta (kamalar), kuma za mu yi qoqari ta hanyar zurfafa tunani a cikin halittar tashi da kuma gano abubuwan da suke a fitirarmu (Dabi\'ar da take 6angaren asalin halittar mu ce) wadanda aka sanya mana su domin wucewa da isa ga hadafi na asali, da kuma sanin abubuwan da suke tattare da mutum da suka bunqasa shi yake da wannan matsayi babba a cikin halittu.

Sannan kuma mu san abin da yake sa dangantaka tsakanin su da halittarmu kuma suke ba mu damar yin amfani da kansu, da kuma qoqari wajen salladuwa da qarfafa su yana dada mayar damu masu qarfi da kasantuwa cikin shiri na musamman, domin qara kammaluwa, saboda kowanne lokaci gwargwadon sanin qarfinmu na ciki wato qarfin ruhinmu da kuma sanin kayan aiki na wajen ruhinmu; to gwargwadon yiyuwar isar mu ga kamala da sa\'ada ta haqiqa zai kasance. Wadda da taimakon Allah madaukakin Sarki hakan zai kasance taku (step) zuwa kammalar kanmu da wasunmu.

Dan haka, Maudhu\'in bahasinmu zai kasance kamar haka, \'MUTUM A MATSAYINSHI NA SAMUWA MAI KARBAR KAMALA\'. Kuma hadafi da fa\'idar bahasin zai kasance kamar haka, \'SANIN KAMALA TA HAQIQA DA KUMA HANYAR ISA GA ITA\'. Kuma hanyar gabatar da wannan bahasi ita ce, BINCIKEN MAHANGOGI NA CIKIN MUTUM (INTERNAL) DOMIN QARIN SANIN BUQATU DA SINADARAN DA SUKE A CIKINMU DA AKA SANYA MANA DOMIN ISA GA KAMALA, DA KUMA ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKA MANA WAJEN KAIWA GA ITA, DA KUMA BINCIKEN SHARUDAN DA ZA MU IYA AMFANUWA DA SU DOMIN WANNAN NUFI NAMU (isa ga kamala).

Kuma za mu yi qoqari wajen gabatar da wannan bahasi da kuma tabbatar da abin da muke buqata, za mu yi amfani da hujjoji da misalai sauqaqa da kuma amfani da mafi sauqin fahimta na daga bayanai domin fito da abubuwan da suka shige mana duhu wadanda suka shafi wannan bahasi. Idan kuma da buqatuwa ko kuma gurin da ya zama wajibi za mu yi ishara ga dalilai na hankali da ruwayoyi masu Dan zurfi. LARURAR (WAJIBCIN) SANIN KAI: Dangane da Samuwar da a fitirar shi yana da son zatin kanshi; to haqiqa dabi\'a ne cewa ya dubi kanshi kuma ya fantsama zuwa ga sanin kamalolin kai da kuma hanyar isa gare su.

Dan haka fahimtar lalurar sanin kai abu ne a fili wadda ba ya buqatar wasu dalilai na qwaqwalwa masu sarqaqiya ko na ruwaya. Ta wannan fuskar, gafala daga wannan haqiqar da ruduwa da abubuwan da ta kowacce fuska ba su da wani tasiri a kamala da sa\'adar mutum, al\'amarine mai ban al\'ajabi kuma karkacewa ce mai zurfi, kuma ya zama wajibi a binciki wannan al\'amari tare da nemo illarshi (sababinshi) da kuma sanin hanyar magancewa da ku6uta daga gare shi. Dukkan yunqurorin mutum, hada da na ilmi da na aiki, yana yin su ne domin tanada ko samar da jin dadi ko alfanoni da kuma masalih na Dan Adam.

To dan haka sanin Shi kanshi mutum da faruwarshi kai da ma kamalolin da mai yiwuwa ya karkata ga su, dole su gabaci dukkan masa\'il, kai in yawaita ma, ba tare da sanin haqiqar mutum da qimarshi ta haqiqa ba; to dukkan wasu bahasosi da yunqurori za su kasance ba su da wata alfanu.

Hatta dagewa da saukakkun addinai da shuwagabanninsu da malaman Akhlaq suke yi akan sanin kai da mayar da hankali ga shi, dukkan wannan shiryarwa ce zuwa ga wannan haqiqa ta Fitra da kuma hankali.

Alqur\'ani mai tsarki, ya danganta ko ya kwatanta Mantuwa ko gafala da kai (self) a matsayin mantawa da Allah kuma Ya sanar da kwatankwacin uqubar wannan sa6o, inda yace:

Ka da ku kasance kamar wadanda su ka manta Allah; sai Shi ma Ya mantar da su kawukansu. (Surar Hashr, aya ta 19).

 

Zamu tsaya a nan, mu hadu a karo na gaba dan ci gaba.