Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

MUMMUNAN ZATO

2016/05/15

MUMMUNAN ZATO

MUMMUNAN ZATO

Wednesday, May 11, 2016 12:29 PM

Haske da duhun rayuwa   Rayuwar mutum gaurayen zuma da madaci ce. Kowane daya daga cikin wahala da nishadi kan iya daukar wani 6angare na rayuwar dan adam a wannan duniyar. Kowane mutum ya kan dandani daci da zaqin rayuwa kuma ya kan zamo abin farautar su saboda mishkilolin rayuwa da masifun ta. Wannan shine haqiqanin al\'amari mara dadi wadda rayuwar mtum take kaiwa da komowa a tsakanin wahala da jin dadi daidai dashi. Mu ba zamu iya jirkita wannan tsarin rayuwa na tun fil azal har ya zamo ya dace da yadda ran mu ke so ba. Amma bayan mun gane haqiqanin wannan rayuwa zamu iya mai da hankalin mu akan kyawawan abubuwan ta kuma mu kau da kanmu daga munanan al\'amuran ta.

Duk zamu iya yin haka a wannan yalwataccen fage wanda ke cike da kyau da hikima wanda kuma ya hada kome da kome na tausasawa ta musamman wadda aka halitta musamman saboda shi. Ko kuma muna iya juya baya mu mance da al\'amuran rayuwa masu haske da haskakawa mu fuskanci al\'amura masu duhu da muni kawai a rayuwa.

A taqaice dai kowa soja ne, malamin kan sa kuma yana iya fuskantar da fikirar sa zuwa duk kusurwar da yaso kuma yana iya rina rayuwar sa da duk irin launin da ya ga dama. Wajibi ne a kan mu, muyi shiri dan fuskantar duk abin da bai dace damu ba wanda yake toshe mana hanyar rayuwa, domin kada mu kasa kintsa kanmu a rayuwa. Idan kuwa ba haka ba to zamu yi qazamar hasarar da ba za mu iya murmurewa ba, mai yiwu wa ne ma mu durqushe a gaban gaggan al\'amuran rayuwa. Mai yiwu wa ne wasu suyi tsammanin cewa idan har dai al\'amura sun kasance suna gudana ta wata fuska dabam, to da sun ci nasara, alhali kuwa ba anan take ba. Babu abin da ya hada rashin nasarar su da yadda al\'amura ke faruwa, illa iyaka dai ya shafi yadda suke

fuskantar al\'amuran ne. Irin hanyar da mutum ya bi ta kan iya samun tasiri a ruhin sa har ta canja shi, hasali ma zai iya cin nasara ta wannan hanyar. Wani daga cikin fitattun marubuta yace: "Tunanin mu da\'iman yana juyawa ne a tsakanin qiyayya da rashin gamsuwa. Duk halin da muke ciki, sai munyi gunaguni, mun koka kuma mun aibata. Dalilin wannan kuka da gunaguni kuwa a zukatan mu yake.

Mu an halicce mu ne ta yadda duk wani abu da bai dace da jikkunan mu da ruhin mu ba, zai azabtar damu. Kullu yaumin ka gan mu, muna buri muna sa rai ga sabon abu sau da yawa ma bama fahimtar abin da muke so. Tsammani muke yi wasu har sun riga sun ci nasara har muke hassada gare su ko muke yi musu qyashi muna azabtar da kanmu. Mu kamar shagwa6a66en yaro muke, wanda zai qaqalo kuka babu gaira babu dalili ya yi ta rusawa, ran mu in yayi dubu sai ya 6aci saboda kuka da kururuwar wannan yaro.

Ba za a huta daga kururuwar wannan yaro ba, har sai mun sa shi ya gane haqiqa, alhali a da babu abin da ya sani illa shirme, sai mu hana shi shirmen da zuciyar sa ke so, domin saboda abin da zuciyar sa ke so ne, ya zama baya ganin wani abu illa mummuna. Dan haka wajibi ne mu bude idonsa ya ga 6angaren alherin wannan rayuwa. Wajibi ne mu fahimtar dashi cewa wanda ya bude idonsa ya duba lambun wannan rayuwa, zai ci nasarar tsinkar furanninta. Wanda kuma ya makance, to babu abin da zai samu illa qayar lambun. Idan muka kau da kanmu daga tsanani da mummunan zato, muka duba da idon basira zamu gane cewa, a kowane zamani, hatta a wannan zamanin namu da ya kama hanyar lalacewa, wanda kuma a kowace sa\'a guda, rayuwarmu take yin juyin waina a cikinsa, lafiyayye da majinyaci kuma suke cudanya, nagari da mugu kuma suke cakuda, za mu ga cewa a ko\'ina cikin lambun wannan rayuwa akwai furanni masu jan hankalin masu kallonsu a kowane zamani".

Tunani yana da tasiri mai zurfi a samun sa\'adar mutum. Hasali ma abu daya kawai da yake da tasiri a sa\'adar mutum shine qarfin hankali da zurfin tunanin sa. Baqon al\'amari wanda ba a saba da shi ba, babban bala\'i ne gagara juriya a gurin mai mummunan zato. Amma mutum mai yiwa rayuwa kyakkyawan zato, sai ya yiwa al\'amarin zaton alheri. Shi ba ya kasa yin gwagwarmaya kome tsananin masifa da baqin ciki, ba ya qetare haddin adalci da daidaito da kame kai da haquri. Wadanda suka yi imanin cewa su karfa ne, kuma qawanyar sharri ta kewaye su dan ta auka musu, to ba zasu ta6a rayuwa ba illa cikin qunci da tsanani da duhu, kuma a al\'amura da yawa za suyi hasarar kuzarinsu da qwazon su a banzar-bazara. Da sannu babu saninsu za su mance da duk wasu baiwa da albarkatun wannan duniya wadanda suka kewaye su.

Wani masani yana cewa: "Duniya da mutum, cin tuwon kishiya suke yi, duk abin da yayi mata shi zata yi masa, idan kayi mata dariya za ta dara maka, idan ka tur6une mata ta tur6une maka, in kayi aiki da tunani sai ta sada ka da masu tunani, in kai mai rangwame ne, mai abota za ka sami mutane kewaye da kai masu qaunar ka, sun bude maka abin da ke zukatansu na taskokin qauna da soyayya".

Ko da yake a zahiri tsanani wani ciwo ne mai radadi amma yana da sakamako na musamman ga ruhi da tunani. Qwazon ruhin mutum ya kan bayyana sosai da sosai a lokacin da yake cikin tsanani. Hankali da ruhin mutum su kan kammala ne a cikin halin sadaukar da kai mai dorewa, da yin qoqari da\'iman da kuma kaiwa da komowa har su kai ga qololuwar kamalar \'yan Adamtaka. Illolin Mummunan zato Mummunan zato yana daya daga cikin cutukan ruhi masu hatsari. Shine tushen kowace hasara da 6ata da fandarewa da ta6ewa.

Shi sharri ne mai ciwo mai azabtar da ruhin mutum. Mummunan tasirin sa kuma baya gushewa daga mutuncin mutum. Radadi da bala\'i abubuwa ne masu saurin ta6a zuciya wadanda zai yiwu su haifar da mummunan zato saboda tunzura da harzuqar zuciya. Irin mummunan zaton da ke kankama a tunanin mutum ta wannan hanyar yana yin tasiri mai muni a zuciyar mutum, wanda ba a amince da shi ba.

Duk wanda madubin ruhin sa ya dunane da qurar mummunan zato, ba zai ta6a ganin kyawun halitta ba. Ba ma wannan kadai ba, hatta alheri ma zai bayyana a gare shi a halin an jirkita kamanninsa, ya zamo cuta da fandarewa, kuma ba zai ta6a iya ganin kyawun aikin kowa ba saboda mummunan zatonsa. Duk wadanda tunaninsu ya rikide ya zamo na sharri, to babu wani kazar-kazar na alheri da zai saura a gare su. Su ne da son ransu suke haifar wa kawukansu irin mishkilolin da suka so kuma suke dakushe qwazonsu da tuntuntuni game da al\'amuran da ba su auku gare su ba tukuna, kuma mai yiwu wa ba za su ta6a aukuwa gare su ba.

Kamar yadda tasirin kyakkyawan zato da hali nagari ke yaduwa su shigi wanda yake kusa, ya raya ruhin kyakkyawan zato a zuciyar sa, to hakanan mummunan zato ya kan harbi na kusa ya zuba masa zugi da radadi da firgita, kuma da sannu zai raba shi da hasken kyakkyawan zato wanda ke haskaka hanyar rayuwa ga masu tafiya. Tasirin mummunan zato ba wai ga ruhi ya tsaya ba kawai, ga jiki ma ya kan yi tasiri har ya jinkirta warkewar cututtuka.

Wani daga cikin manyan likitoci yace: "Yin jinyar mutum mai munana zato ga kowa da kome, yafi ceto wanda ya jefa kansa a rijiya da nufin kashe kansa, wahala. Bayar da magani ga wanda da\'iman yake cikin qunci da damuwa a rayuwa kamar zuba ruwa ne a cikin tafasasshen man da ke kan wuta. Kafin wani magani yayi amfani, babu makawa sai zuciyar marar lafiyan ta amince kuma ya nutsu".

Wanda cutar mummunan zato ta kama shi za a gan shi quru-quru yana qauracewa da tsoron zama tare da jama\'a. Saboda da irin wannan hali abin qi, da sannu zai wargaza irin shirin da ke zuciyarsa na ci gaba, kuma da sannu rayuwarsa za ta zama ba abar yarda ba. Mummunan zato na daya daga cikin abubuwan da ke sa mutum ya kashe kan sa. Qudirar aniyar kashe kai galibi ta kan tsiro ne daga mummunan zato dangane da rayuwa. Idan muka duba halin da jama\'a ke zama tare da juna a al\'umma, za mu ga cewa yawancin abubuwan da ke aukuwa a junansu na rashin jituwa, mummunan zato ba tare da yin bincike da tunani bane yake jawo su. Duk da cewa su masu rauni ne wajen aunawa da hukumta al\'amari, amma sai kawai su yanke wa wasu hukumci kafin ma su gane kai da gindin lamari, sai kawai su gaskata abu ba tare da lissafi ba, za a iya gane manufofin su ta irin maganganunsu.

Wannan aibi mai girma ya kan jawo lalacewar hadin kai. Har ila yau ya kan hana mutane amincewa da junansu, ya 6ata dabi\'unsu nagari hatta ruhinsu. Da yawa qiyayya da gaba da juna masu cutar da jama\'a da al\'umma baki daya, mummunan zato sa6anin haqiqa da gaskiya ne yake jawo su. Mummunan zato ya kan bazu a tsakanin kowane 6angare na mutanen al\'umma, wani lokaci ma har ya kan kama tunanin malamai da masana falsafa.

A tarihin al\'ummu daban-daban za mu sami wasu malamai sun yi mummunan kuskure saboda mummunan zaton su. Maimakon su amfani al\'ummar mutum da ilminsu sai suka gina ra\'ayoyinsu akan asasin suka da qididdigar aibobin tsarin halittar duniya, sai suka zubawa ruhin al\'umma gubar wannan ra\'ayi nasu da manxiqinsu na kuskure, suka dinga kushe asasin kyawawan halaye da aqida suna izgili da su.

Tsoro da baqin cikin da wasunsu suke yi game da yawan jama\'a da talauci da bala\'i ya kai su hatta ga halatta duk wani abu mai yiwa zuriyar mutum barazana, sun halatta yaqe-yaqe da zubar da jini. Idan da mutane sun daka ta rawar irin wadannan, to da a yau ba a sami ko alamar ci gaban mutum ba. Abul Ala Almauri yana daya daga cikin masana falsafa masu mummunan zato. Shi ya kasance yana ganin cewa rayuwa baki dayanta wahala da azaba ce, ya kuma kasance yana haramta saduwa da mata da haihuwa, domin wai zuriyar mutum ta qare, kada na baya su sha azaba. Yayin da yazo mutuwa sai ya yi wasiyya da a rubuta wasu baitoci daga cikin waqensa a kan kabarinsa kamar haka: "Wannan shine zunubin Babana gare ni. Ni kuwa ban yiwa kowa zunubi ba.

Gargadi

Alqur\'ani ya bayyana qarara cewa mummunan zato zunubi ne, kuma ya gargadi musulmi da suyi nesa da yi wa junansu mummunan zato. "Ya ku wadanda suka yi imani, ku nesanci yawancin zato, domin wani zaton zunubi ne". (surar Hujuratu: 12)

Manzon Allah (SAWA) yana cewa: "Jinin musulmi ga musulmi haramun ne, da dukiyarsa, da kuma yin mummunan zato game da shi". Sahih Muslim, Kitabul Birri, babi na 32, da Musnad Ahmad Juz\'i na 2, shafi na 277, Juz\'i na uku shafi na 491 da Tirmizi Kitabul Birri babi na 18.

Kamar yadda musulunci bai yardar wa wani haka kawai sarmadan ya dauki dukiyar wani ya bawa wani ba, kazalika ko kadan bai yarje wa kowa ya munana zato ga wasu ba tare da tabbatar da gaskiyar al\'amarinsu ba. Ya zo a Nahul Balagha shafi na 174 cewa Imam Ali (AS) yana cewa: "Yanke wa wanda aka amince da shi hukumci a kan zato ba adalci ba ne".

Har ila yau kuma yayi kyakkyawan bayani a kan irin illoli da 6arna da cutarwa daban-daban da mummunan zato yake yi wa zuciya da ruhi, inda yake cewa: "Ka kiyayi kanka da mummunan zato, domin mummunan zato yakan 6ata ibada kuma ya kan qara yawan laifi". littafin Gurarul Hikam shafi na 154

yin mummunan zato ga mutanen qwarai wani nau\'i ne na zalunci. Inda yake cewa: "Munana zato ga mai aikin qwarai shine mafi sharrin laifi, har wa yau kuma shine zalumci mafi muni". Littafin Gurarul Hikam shafi na 434

Aiki da mummunan zato a tsakanin abokai kuwa ya kan raunana dangantaka kuma ya kan zamo sanadin ta6ar6arewar abota da jawo yanke qauna. Imam Ali (AS) yana cewa: "Duk wanda mummunan zato yayi galaba a kan sa, to babu sauran zaman lafiya tsakanin sa da abokin sa". littafin Gurarul Hikam shafi na 698

Bayan qazamar illar da mummunan zato yake yi wa hali da rayuwar mai mummunan zaton, har ila yau ya kan iya shafar halaye da zukatan wasu mutane. Idan har aka yi wa wani zargi alhali bai ji ba bai gani ba, to wannan yana iya sa shi ya kufula ya qauracewa halayen qwarai ya fandare ya shiga fasadi da aikata miyagun ayyuka da rashin mutunci. Imam Ali (AS) ya ci gaba da cewa: "Mummunan zato yana 6ata al\'amura sa\'annan ya jawo ashararanci". littafin Gurarul Hikam shafi na 433

Mummunan zato da zargi sukan yi sanadin 6acin ayyuka kuma su jawo lalata da qasqanci.

Dr Marden ya rubuta cewa: "wasu attajirai su kan yiwa barorin su mummunan zato har su zarge su da yi musu \'yan sace-sace a kantunansu alhali kuwa ba haka ba ne. A qarshe kuwa sai yaran nasu su tsiri yi musu satar kamar yadda aka zarge sun. Dalili shi ne domin mummunan zato ko da ba a furta shi da baki ba ya kan ratsa zuciya ya 6ata ta, har ya kai su ga yin satar". Littafin Pirozi Fikr

Imam Ali (AS) yana cewa: "Ka kiyayi zargi a inda bai dace ba, domin yin haka ya kan sa cuta ga mai lafiya, kuma ya sa kokwanto ga wanda ba shi da aibu." Littafin Gurarul Hikam shafi na 152

Haka nan ya sake cewa wanda ya kamu da wannan cuta ta mummunan zato, to shi kam ya yi sallama da kwanciyar hankali. "Mai kokwanto ba ya ta6a samun lafiya." Littafin Gurarul Hikam shafi na 835

Dokta Carl yace: "Akwai wasu dabi\'u wadanda suke raunana qarkon rayuwa. Al\'adar kushe kowane abu, da yin mummunan zato ga komai, kiciciyar halaye ce mai daddage zuciyar mutum har ila yau kuma tana iya 6ata ayyuka ta nakasa ga6o6i." Littafin Rah wa rasm zendegi.

Dokta Marden kuma yace: "Mummunan zato ya kan ta6a lafiyar jiki kuma ya kan 6ata halayen qwarai. Lafiyayyiyar zuciya har abada ba ta tsammanin sharri, da\'iman alheri take saurare domin ta san cewa alheri har abada ba ya shudewa. Sharri kuwa ba wani abu ba ne illa rashin alheri, kamar yadda duhu ba wani abu ba ne illa rashin haske. Saboda haka ku kama hanyar neman haske domin yana kore duhu daga zuciya." Littafin Pirozi Fikr

Mutumin da zuciyarsa ta cika da mummunan zato zai kasance yana tsoron mutane. Imam Ali (AS) yana cewa: "Wanda ba shi da kyakkyawan zato zai kasance yana jin tsoron kowa." Littafin Gurarul Hikam shafi na 712

Dokta Farmar kuma ya ce: "Duk mai qin bayyana ra\'ayinsa ko furta abin da ke zuciyarsa a cikin taro alhali kowa yana bayyana manufarsa, da kuma wanda yake qin bin manyan titunan cikin gari, yake qauracewa matattarar jama\'a dan tsoron gamuwa da \'yan uwa da abokan arziqi, ba wani abu ba ne yake sa shi haka ba illa wahami da mummunan zato." Littafin Raz khushbakhti.

Bacin rai da tsanani su kan taru su cika zuciyar mutum har su kai shi ga halin mummunan zato ba tare da ya yi la\'akari ba. Imam Ali (AS) yana cewa: "Zukata suna da wasu mugayen qudurori wadanda hankula suke jin tsoron su." Littafin Gurarul Hikam shafi na 29

Dakta Haleem yace: "Mutanen da ba su amince da kansu ba sun fi saurin harzuqa. Dan tsananin da bai taka kara ya karya ba, sai ya dame, sa\'annan su dinga tuna shi dindindin har sai ya yi musu illa qwarai ba tare da sun sani ba. Sai su zamo masu qunci ko dacin rai, ko masu mummunan zato, kuma ba za su iya gane sanadin wannan cuta da ta qulle zuciyarsu ba. Munanan ra\'ayoyi masu cutarwa a 6oye suke a cikin zukatan mu, kuma ba sa bayyana a cikin sauqi. A wani qaulin kuma, mutum a bisa dabi\'a ba ya qaunar abubuwa marasa dadi. Dan haka ba ya son in ya mance da su ya tuno su. Amma maqiyin 6oye, wanda ba zai bar qulla mana makirci da danyen aiki ba, sai ya yi ta juya zukatanmu da ayyukanmu da halayen mu yadda yake so. Sai mu dinga aikata wasu ayyuka ko fadar wasu maganganu wadanda suke ba mu al\'ajabi domin mu da kanmu da kuma sauran jama\'a mun san cewa ba a bisa tafarki suke ba. Idan muka koma cikin hankalinmu muka yi nazari sai mu gane cewa sakamakon munanan ra\'ayoyinmu da ke qulle a cikin zukatanmu ne." Littafin Rushd shakhsiyyat

Mutum mai mummunar dabi\'a da\'iman ya kan sanya kansa ma\'auni ne da zai dinga auna dabi\'ar wasu kuma irin munanan halayen da yake da su yake gani a jikinsu. Imam ali (AS) yana cewa: "Asharari ba ya zaton alheri ga kowa, domin ba ya ganin kowa sai da irin dabi\'arsa." Littafin Gurarul Hikam shafi na 80

A lokacin da Manzon Allah (SAWA) ya yi hijira daga Makka zuwa garin Madina sai wani mutumin Madina ya nufo shi ya ce masa: "mutanen garin nan mutanen kirki ne dan haka ya yi kyau qwarai da ka qaurato zuwa gurinsu." Sai Manzon Allah (SAWA) yace: "kayi gaskiya." Daga baya kuma sai wani ya lalla6o ya ce wa Manzon Allah (SAWA): "mutanen garin nan masharranta ne, inama ba ka yiwo hijira ka zo cikinsu ba." Sai Manzon Allah (SAWA) yace: "ka yi gaskiya." Sai wani sahabi ya tambayi abin da ya sa ya ce duka sun yi gaskiya. Sai ya ce: "kowane daya daga cikin su ya fadi yadda zuciyarsa take ne, dan haka kowannensu ya yi gaskiya." Abin nufi kowane daya daga cikin su ya fadi gaskiya ne game da abin da ke cikin zuciyarsa.

Ya kamata a gane cewa mummunan zato ta6ewar tunani ce da kuma kafewa a kai, abin da aka haramta a nan shi ne yin aiki da mummunan zaton. Domin tunani da wahami al\'amura ne da ke cikin zuciya da qwaqwalwa, mutum kuma ba shi da iko a kansu, kuwa ba shi da mafita kenan kuma babu wani takalifi game da su a shari\'a. Kamar yadda aka bayyana a can baya cewa wannan cuta tana sabauta qunci da rashin ribar rayuwa lalle a yi nazari cikin tsanaki dan a gano sanadinta. In har an gano abin da ke jawo mugun zato sai a magance shi ta hanyar sanadin.

Mun tsamo muku wannan maqala ne daga rubututtukan fitacce malamin Tarbiyan nan wato marigayi Sidi Mujtaba Musawi Lari (Allah Ya yi mashi rahma).