Languages فارسی فارسى درى English اردو Azəri Bahasa Indonesia پښتو français ไทย Türkçe Hausa Kurdî Kiswahili Deutsche РУС Fulfulde Mandingue
Scroll down
Darusan Akhlaq

KYAKKYAWAN ZATO

2016/04/19

KYAKKYAWAN ZATO

KYAKKYAWAN ZATO

Tuesday, April 19, 2016

2:34 PM

Dan Adam yana buqatar kwanciyar hankali fiye da komai a wannan rayuwa da take cike maqil da rudani. Duk wanda bai kare kansa da wannan makami ba to kuwa yaqi ya ci shi an gama. Duk yayin da nauyin rayuwa ya qara yawa sai wannan buqatar ma ta qara tsanani daidai wa daida. Dan haka lalle ne mu nema wa kan mu mafita daga rudu da ribibin rayuwa, mu kai ga tudun mun tsiran natsuwa da kwanciyar hankali.

Duk wani qoqarin neman kwanciyar hankali ta hanyar dukiya ko qarfi ko muqami shirme ne kuma za a gama a tashi a tutar babu. Dalili kuwa shine zuciya itace tushen alheri, kazalika kuma ita ce tushen sharri. An hakaito cewa Imam Ali (AS) yana cewa:

Kana zato kai halitta ce qarama,

Alhali ka qunshi halitta mai girma,

Cutar ka a jikin ka da zuciyar ka take,

Maganin ka a gare ka da zabin ka yake.

Tunda yake cuta da magani a zuciya suke, to ba za a taba cim ma buri ba sai ta hanyar zuciyar. Domin ita ce take da qarfin badini a jikin mutum. Duk wata hanyar jin dadi da kayan alatu da aka riqe su don a cim ma wannan buri, masu gushewa ne kuma ba za su kai mutum ga kwanciyar hankali mai dorewa ba. Wadar zuci da kyawawan dabi\'u wadanda ba sa gushewa sune kawai za su iya kange mutum daga kame-kamen abubuwa masu gushewa.

Apiktatus, mashhurin masanin falsafa na qasar Japan yace:

"Wajibi ne mu sanar da mutane cewa ba za su iya samun farin ciki da kwanciyar hankali a gurin da suke tsammanin su ba. Kwanciyar hankali ba a qarfi da iko take ba. Mirad da Agluis sun kasance suna da qarfi ga kuma mulki, amma ba su samu kwanciyar hankali ba. Kwanciyar hankali ba a tarin dukiya take ba. Croesus ya kasance ya mallaki dimbin taskokin dukiya amma bai sami kwanciyar hankali ba. Har ila yau kwanciyar hankali ba a qarfin daula da girman muqami take ba. Sarakunan Romawa sun kasance masu qarfin mulki amma duk da haka basu sami kwanciyar hankali ba. In an hada duk wadannan abubuwa duk ba za su samar da kwanciyar hankali ba. Neru da Sandnapal da Aghamnin mutane da suka kasance sun mallaki dukiya da mulki da kuma shuhra, amma da\'iman suna gunjin kuka don sun san cewa in 6acin rana tazo zai yiwu ayi kaca-kaca da su. Saboda haka kowa ya nemo kwanciyar hankalin sa a zuciyar sa da qwaqwalwar sa."

Lalle ne mu gane cewa magance wasu matsalolin na yau da kullum da yawaita hanyoyin holewa na zamani ba za su ta6a samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya ba. Domin ba su isa su rage dacin rayuwa ba sai dai ma su qara sababbin rudani da qunci da kuma damuwa.

Saboda haka ya zama tilas muyi aiki da qwaqwalwar mu domin mu fice daga duhun girgijen da ya lullu6e zukatan mu. Aiki da qwaqwalwa shine ya kai mutum ga cin nasara a kowane 6angare na rayuwa, har ya gyara komai dan amfanin kansa, saboda haka yana iya kaishi ga samun kwanciyar hankali. Kwanyar mutum ba ta da na biyu wajen tasiri a rayuwa. Itace za ta gyara kuma ta haskaka rayuwar dan adam.

Lafiyayyar qwaqwalwa mai fahimta ita ce tushen alheri. Za ta daukaka mutum ta fifita shi sama da duniya da abin cikin ta. Ra\'ayoyin mutum mai fasaha su kan kange shi daga fadawa cikin kogin baqin ciki. Duk wanda qwaqwalwar sa ta samu kyakkyawar tarbiyya, ta goge ta kankama a zatin sa to ba shakka zai iya tsayawa ya fuskanci duk wata arangama. Zai zamo tamkar tsauni, ruwa ba ya yin awon gaba da shi, iska kuma ba ta girgide shi.

Wajibi mu shirya wani tsari da zai zamo ma\'aunin shigi da fici a gare mu. Har ila yau kuma ra\'ayoyi sahihai su zamo suna mana ja-gora zuwa ga bain da yafi inganci kuma su zama sun qarfafa ruhin mu domin magance duk abin da yake jawo mana qunci domin kada mu tsunduma jirgin ruwan mu cikin ambaliya da ganganci.

Wani daga cikin masanan Turai yana cewa:

Mai yiwuwa a za6e ba za mu iya za6o \'yan qalilan masu irin dabi\'un mu ba, ko kuma wadanda muka dace da su ta wata fuskar, amma ai muna da \'yancin ra\'arayi tunda yake hankali shine alakali, mu kuma mune masu zartar da abin da muka so. Kuma babu wasu dalilai ko wani hali ko tasiri da muke gani a zahiri da za su tilastawa hankali ko tunaninmu don mu za6i abin da ba ma so. A wani qaulin kuma muna iya cewa tunanin mu shine mai jan mu ya kai mu duk inda yaso. Dan haka kada mu kuskura mu sabar wa kan mu mummunan tunnai. Kada mu sake mu sabar wa hankalin mu bin mummunan ra\'ayi har ya tsunduma mu a cikin bala\'i. Lalle koyaushe mu kasance cikin tunanin kamala ba tawaya ba na kyakkyawan fata da kuma kyakkyawar manufa domin kowace nasara da sa\'ada ta hanyar lafiyayyen tunani kawai ake samun ta."

 

Sakamako da ribar kyakkyawan Zato

Kamar yadda cututtuka iri dabam-dabam suke nakasa jiki, haka miyagun dabi\'u da munanan sifofi suke lalata nutsuwa da tunani. Duk da qarfin da kwanya take da shi tana buqatar agajin kyawawan dabi\'u. Mutum ya kan ji farin ciki idan yana da kyawawan dabi\'u, kazalika kuma idan dabi\'un nasa suka zama bai daya da tunanin sa. Saboda haka wajibi ne mutum yayi himma ya kankare munanan dabi\'un da suka lullu6e rayuwar sa ya musanya su da kwanciyar hankali da nutsuwa.

Daya daga cikin abubuwan da ke ba da kwanciyar hankali shine fata na gari a rayuwa da kuma yarda da jama\'a. Fata na gari da kyakkyawan zato ga mutane suna samar da nutsuwa, sa6anin mummunan fata da mugun zato ga jama\'a, wadanda ke dushe tunani su tsimburar da kamalar sa. Fata na gari a rayuwa kamar haske ne a cikin duhu, yana fadada tunani kuma ya qara wa mutum son alheri, ta haka har zai ci gaba a fahimtar sa game da rayuwa da ra\'ayinsa game da ita. Sai ya gane kyawun rayuwa da dadin ta kuma ya dinga ganin mutane da daraja yana mutunta su sosai. Sakamakon haka sai damuwar sa ta ragu, tsammanin alherin sa ya qaru, kuma dangantakar sa da jama\'a ta qara qarfi sosai a zuciya da kuma a zahiri.

Babu wani abu da ke fitar da mutum daga qunci da damuwar rayuwa kamar fata na gari. Duk wanda yake da wannan za6a66en hali na qwarai ba wai kawai a lokacin zaman lumana ne yake da nutsuwa ba, a\'a ko da a cikin arangamar al\'amuran yau da kullum ne yakan kwantar da hankali ya bi komai cikin nutsuwa ya warware shi ta hanyar aiki da hankali cikin sauqi. Kuma shi da\'iman yana cikin annashuwa ne da nutsuwa da kwanciyar hankali.

A rayuwa larura ne mutun ya yi abin da zai sa jama\'a su amince da shi. Dole ne fata na gari ya yawaita a tsarin zaman tare wajen yardar da mutane. Jin hakan kuwa na tasiri a samun sa\'adar daidaiku da kuma al\'umma baki daya. Amincewa da juna a tsakanin jama\'a za ta jawo ci gaban al\'umma, alhali rashin amincewa kuwa zai jawo dakushewa da lalacewar al\'umma. Duk yayin da dangantakar jama\'a ta qara qarfi ta qara kyau to la-budda ci gaban al\'ummar ma zai qara qaimi ya ha6aka. Babbar ribar fata na gari ita ce hade kan jama\'a da sa taimakekeniya da yarda da juna a tsakanin su. Idan aka assasa zama da juna a bisa alaqar zukatan juna, amincewa da kuma yiwa juna kyakkyawan zato, to haqqan za a zauna cikin farin ciki kuma a yi zaman lafiya. Amma matuqar babu kyakkyawan zato ga juna a tsakanin jama\'a zukata kuma suka cika da shakku da zargin juna, ba zai yiwu a sami taimakon juna a tsakanin su ba, hasali ma sai suyi ta muzgunawa da cakar juna babu gaira babu dalili. Al\'ummar da ke cike da irin wannan hali kuwa holoqo ce ba ta da wani abin kuzo ku gani irin na sauran al\'ummu.

Wani malami yace:

"Kyakkyawan zato yana daga imani, babu wani aiki da zai yiwu idan babu imani da kyautata zato."

Gwargwadon yadda mutum ya amince da mutane suma kimanin yadda za su amince da shi ke nan, domin yadda kayi haka za a yi maka, a kowace al\'umma ne kuwa. Amma kada mu manta da cewa akwai wagegen bambanci tsakanin fata na gari da yin kyakkyawan zato ga wasu. Ko kadan ba kyakkyawan zato bane haka kawai mutun bai san wani ba ya miqa masa wuya a rana tsaka, ya bi duk abin da ya fada sau da qafa ba tare da bincike da aunawa ba. Har ila yau bai kamata mu yi wannan zato ba ga wanda ya shahara wajen aikata sa6o a bayyane. A taqaice dai ba koyaushe ne ake yi wa kowa kyakkyawan zato a kowane hali ba. Mutum mai kyautata zato da yiwa ayyukan mutane kyakkyawar fassara ba wai galantoyi ba ne, da\'iman ya na lura ne da kyakkyawan qarshen al\'amura. Dan haka yana taka tsantsan a kaiwa da komowarsa kuma yana kyakkyawan nazari da tunani a ayyukan sa.

Musulunci yana umarni da kyakkyawan zato

Addinin musulunci ya umarci Musulmi da su yiwa junan su kyakkyawan zato kuma su yiwa ayyukan mumini kyakkyawar fassara wadda ta dace da shari\'a. Bai halatta ba wani ya dauka cewa wane fasiqi ne matuqar bai tabbatar da qaqqarfar hujja ba.

Imam Ali (AS) yace:

"Ka dauki al\'amarin dan uwanka a matsayi mafi kyawu har sai wani abu da zai sa ka janye ya bayyana a gare ka, kada ka yi mummunan zato ga kalmar da ta fito daga bakin dan uwan ka alhali za ka iya yi mata kyakkyawan zato."

Littafin Jami\'us Sa\'adat, Juz\'i na 2, shafi na 28

Yi wa juna kyakkyawan zato yana qulla qauna a tsakanin jama\'a kuma ya samar da hadin kai a tsakanin su. Shugabannin musulunci sun yi bayanai iri-iri dangane da sakamakon kyakkyawan zato. Imam Ali (AS) yana cewa:

\'Duk wanda ya yi kyakkyawan zato wa mutane to za su so shi."

Littafin Gurarul Hikam

Dokta Marden yace:

"Idan za kuyi abota da wani, to ku yi qoqari ku dubi kyawawan halayensa da dabi\'unsa na qwarai kawai. Sa\'annan kuma kuyi qoqari ku mutunta wadannan halaye nasa a zuciyar ku. Idan har kuka yarda da wannan wasiyya tawa kuka riqe ta a zuciyar ku to za ku yi zaman lafiya da kowa kuma kowa zai yi sha\'awar qulla abota da ku."

Littafin Pirozi Fikr

Kyakkyawan zato da amincewa da jama\'a na iya canja hatta tunanin waxanda suka dulmiye a cikin zunubi ma. Yazo a littafin Gurarul Hikam shafi na 378 cewa Imam Ali (AS) yana cewa:

"Kyakkyawan zato yana kuvutar da wanda ya dulmiya a cikin aikata zunubi."

Dakta Dale Carnegie yace:

"Na gana da shugaban qungiyar masu Hotel wadda aka assasa ta a shekarar 1885. Adadin Hotel-hotel din da ke cikin wannan qungiya, Ashirin da shida ne, ana gudanar da ayyukan wadannan hotelolin ne ta wata hanya ta musamman da ake kira, \'Mu\'amalar ban girma\', a wadannan hotelolin ba a ke6e wani mutum na musamman don yin lissafin kudin abinci ba. Duk mai son abinci zai shiga ne kai tsaye ya fadi irin wanda yake so kuma a bashi, illa iyaka shine zai duba bill din kudin ya ga yadda ya kama bayan ya ci ya sha, kuma in ya zo fita sai ya ba da kudin ga mai lura da asusu, ya yi tafiyar sa ba tare da wani ya yi masa qididdiga ba cewa shin daidai ya biya ko a\'a.

Sai na yi wuf nace wa shugaban wannan qungiya, tabbas dai kuna da dan sandan ciki ko? Domin ba zai yiwu ku amince da duk mutanen da ke zuwa nan dan cin abinci ba. Sai shugaban ya kada baki yace da ni, Af! Ai mu ba ma gadin masu cin abinci domin mun yi imani da cewa aikin da muke yi gabadayan sa mai kyau ne, ba don haka ba, da ba mu ci gaba da gudanar da shi haka har na shekara hamsin ba. Duk masu zuwa cin abinci a nan sun san cewa ana yi musu ma\'amalar ban girma ta masu karimci, dan haka kowa daga cikin su, faqirin su da mawadacin su, 6arawon su da ma6arnacin su qoqari yake ya ga ya zamo daidai da kyakkyawan zaton da ake yi masa a nan."

Mista Louis liktan dabi\'un \'yan Adam yace:

"Idan kuna tare da qidahumin mutum mai ta6argaza a shigi da ficin sa, idan har kuna so ku dawo da shi kan hanyar alheri to kuyi qoqari ku sa ya fahimci cewa kun amince da shi kuma ku yi masa mu\'amalar mutunci da karimci, in har kun yi haka, da sannu za ku ga yana rikedewa dan ya zamo amintacce saboda amincewar da ku ka yi da shi. Har ila yau kuma zai yi ta fadi-tashi dan ya dace da zaton da kuke yi masa na alheri da mutumci."

Littafin A\'iyne Dostyabi

Dokta Gilbert Roben ya rubuta cewa:

"Ku gaskata yara. Wato kuyi mu\'amala da su tamkar ba su ta6a aikata wani kuskure ba. Abin nufi shine ku mance da abin da ya riga ya wuce. Ku dorawa gantalalle daga cikin su, ko laqwasono, ko qazami a taqaice dai duk wani mai baudewa daga sahun jama\'a a cikin su, a dora masa muhimmin aiki sa\'annan a lura da shi, a qarshe za a ga ya gyaru ya zama na gari. Abin da zai jawo haka kuwa shine, yarda da aka yi da shi. Amincewa da kyautata mu\'amala suna iya kawar da cikas din da ke iya hana ruwa gudu. Dan haka, wasu ayyukan kato6ara gyaran gangar auzunawa ke jawo su."

Yal  Bint yana ganin cewa babu wata hanyar da za a iya raba yaro 6arawo da dauke-dauke illa a tila masa amanar kudi, talala6o (rago) kuma a nannaga masa aiki daidai qarfin sa ko ya zama mai kuzari.

Kyautata zato yana kwantar da hankalin mutum.

Imam Ali (AS) yana cewa:

"Kyakkyawan zato hutun zuciya ne kuma ku6utar addini ne."

Littafin Gurarul Hikam shafi na 376

Kyakkyawan zato magani ne mai warke zulumin al\'amuran rayuwa na yau da kullum. Ya zo a littafin Gurarul Hikam shafi na 377 cewa Imam ali (AS) yana cewa: "Kyakkyawan zato na rage zalama".

Dr. Marden na cewa:

"Babu wani abu da zai sa mu ga kyawun rayuwa kuma ya rage mana dacin ta, ya buda mana hanyar muwafaqa kamar kyakkyawan zato. Ku ji tsoron mummunan zato kamar yadda ku ke tsoron cututtuka da jafa\'i. Ku bude qwaqwalwar ku ga kyakkyawan zato za ku yi al\'ajabin yadda za ku tsira daga munanan tunane-tunane cikin sauqi".

Littafin Piroz Fikr

Lalle ne mu\'amalar musulmi ta zamo ta yi nesa da mugun fata da mummunan zato a tsakanin su. Dan hakane Imam Ali (AS) yake wasici, inda yake cewa a kyautata mu\'amala a tsakanin juna. Matuqar jama\'a suna yi maka kyakkyawan zato; to kada ka aikata abin da zai sa su ga tsiraicin ka har ka basu kunya.

"Duk wanda ya dogara da kai yana maka tsammanin alheri to lalle yayi maka kyakkyawan zato, dan haka kada ka sa6awa zaton sa".

Littafin Gurarul Hikam,  shafi na 680

Har ila yau ya nuna cewa zato alqalin hankali ne, inda yace;

"Zaton mutum shine mizanin hankalin sa, aikin sa kuma shine kyakkyawan shaida a kan asalin sa".

Littafin Gurarul Hikam shafi na 474

Idan zaton wani game da mutane mummuna ne, to babu shakka hankalin sa ma haka yake. Kore mummunan zato game da wani daga zuciya kyakkyawan dalili ne da ke nuna qarfin zuciyar wanda ya aikata hakan, Imam Ali (AS) yana cewa:

"Wanda yayi watsi da mummunan zato game da wani, to hankalin sa lafiyayye ne, zuciyar sa kuma nutsattsiya ce".

Litaafin Gurarul Hikam  shafi na 676

Samuel Smile yace:

"Ya tabbata cewa duk wani mai qarfin himma da yalwar qirji, farin ciki da tsammanin alheri ne dabi\'ar sa a rayuwa. Da\'iman yana lura da kowa cikin nutsuwa da sanin ya kamata. Komai tsananin duhu ma\'abota hankali suna ganin haske su kuma bi shi, kome rintsi da rikitarwa kuma suna rarrabe alheri su bi shi. Dan haka su, kome bala\'i da musiba sai su qara qarfi, kome qunci da baqin ciki kuma sai su qara dauriya da fahimta da ilmi. Dabi\'a irin wannan alheri ce da wadda ta kamata sahibin ta ya riqe ta da kyau. Masu irin wannan dabi\'a koyaushe suna cikin annurin fuska da fara\'a, zukatan su kuma suna cike da haske tamkar wata daren sha biyar. Duk inda suka fuskanta sai su haska shi tarwai ya rikida, ya zamo irin launin da suka so daga cikin launuka".

Imam sadiq (AS) ya nuna cewa kyautata zato, haqqin musulmi ne akan musulmi dan uwan sa, inda yace:

"Yana daga haqqin mumini akan mumini... kuma kada ya qaryata shi".

Littafin Usulul kafi, Juz\'i na 1, shafi na 394

Qarfin imani shine abu mafi muhimmanci wajen samar da kyakkyawan zato. Idan har mutane suna da cikakken imani to tabbatacce ne cewa za su amince da juna. Cutar rashin isasshen imani itace take tum6uke kyakkyawan zato ta dasa mummunan zato a gurbin sa. Musulmi na qwarai mai cikakken imani mai zaton alheri mai tawakkali, duk yayin da ya fahimci cewa ya gaza, nan da nan sai ya mayar da al\'amarin sa ga Allah, ya riqe shi da tsarkakakkiyar zuciya alhali yana riqo da halaye na qwarai, har ya kai ga samun canji cikin sauqi.